Rundunar yansandan jihar Borno ta sanar da ƙarfafa matakan tsaro gabanin ziyarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zuwa jihar ranar Asabar. Rundunar ta ce an ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a lokacin ziyarar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a Maiduguri ranar Asabar, ya bayyana cewa Kwamishinan yansanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya tanadi ingantaccen tsarin tsaro da ya haɗa da jami’an ’yansanda na yau da kullum, da rundunonin musamman, masu sa ido, da jami’an kula da taron jama’a, da sashen kunce bama-bamai (EOD).
- Sojoji Sun Yi Kuskuren Kashe Mutanen Gari A Borno
- Tinubu Zai Ziyarci Borno Ranar Asabar Don Ƙaddamar Da Aiyuka
Rundunar ta kuma sanar da cewa wasu hanyoyi, musamman hanyar da ke hade Titin Filin Jirgin Sama zuwa Titin Shehu a Maiduguri, na iya fuskantar takaita zirga-zirgar ababen hawa ko karkatar da su na ɗan wani lokaci domin sauƙaƙa motsin manyan baki da kuma kare lafiyar jama’a. An shawarci direbobi da mazauna yankin da su yi haƙuri tare da bin umarnin jami’an tsaro.
Rundunar ta tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi kafin, da yayin, da kuma bayan ziyarar Shugaban Ƙasar. Haka kuma ta yi kira ga jama’a da su ba da haɗin kai, su kasance masu sa ido, tare da bayar da rahoton duk wani motsi ko lamari da ake zargi ga ofishin ’yansanda mafi kusa ko ta hanyoyin gaggawa da aka tanada.














