Ministan Ma’aikatar kula da sufurin Jiragen sama Hadi Dirka ya shelanta cewa, Gwamnatin Tarayya, za ta kakaba wa Kamfanonin Jiragen sama na kasar da ke shigo wa cii kasar, Takunkumi saaboda yadda suke sayar da Tikitin ga matafiya kan Dalar Amurka.
Hadi ya ce, rahotannin bayanan sirri sun nuna yadda wasu masu kamfanonin ke yin amfani da naira inda suke canza kudin Tikitin zuwa takardar Dalar Amurka.
Don su sayar wa da fasinjojin Tikitin a kan Dalar Amurka, inda ya sanar da cewa, aikata hakan, savawa dokolin Nijeriya ne.
Hadi ya kuma umarci hukumar kula da sufurin Jiragen sama y kasa wato NCAA da ta yi maganin irin wadandan kamfanonin na Jeragen sama na kasar waje da aikata wannan lafin, inda ya kara da cewa, wasu daga cikin irin wadandan Kamfanonin har ta kai ga suna toshewa kamfanonin cikin kasar nan da ke sana’ar samar da Fasfot da biza ga matiya kafofin su sadarwa domin su damar sayar da Tikitin a kan farashin Dalar Amurka.
A cewarsa, kamfanonin na ketare sun samu ribar sama da Dala Biliyan 1.1 daga Nijeriya a 2016 a lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da Dala Miliyan 600 na abinda ta gaza daga gun Gwamnatin da ta gabatada, inda ya kara da cewa, har ila yau, an fitar da sama da Dala Miliyan 65 ga kamfanonin na Jiragen a cikin wannan shekarar.