Ranar Lahadi ta makon da ya gabata ne Barista Jamilu Ayuba Mairuwa Shugaban kungiyar magoya bayan dan takarar gwamnan Jihar Katsina na APC Dakta Dikko Umar Radda da aka fi sani da Faskari Connect, ya jagoranci gudanar da gaggarumin taronta na farko a garin ‘Yankara a karamar hukumar Faskari jihar Katsina.
Ya kuma kaddamar da shugabannin kungiyar tun daga matakin karamar hukuma, har ya zuwa na mazabu.
- NIS Fara Sintirin Fatattakar Baƙin Haure Mai Taken “Saukar Shehu” A Bayelsa
- Sin Da Rwanda Sun Tsawaita Yarjejeniyar Hadin Gwiwa A Fannin Kiwon Lafiya Na Tsawon Shekaru 5
Wadanda aka kaddamar a matsayin shugabannin kungiyar a matakin karamar hukumar Faskari sun hada da,Shugaba Alhaji Hassan Umar, Sakatare Lawal Sani Yankara, Ma’aji Bishir Yahaya Sheme, Shugaban matasa Bala G Garba Mairuwa,Shugabar mata Aisha Shehu Faskari, mataimakiyar Shugabar Hadiza Tanimu Daudawa,Jami’ar mulki Aisar Isah Barau,Sakataren tsare- tsare Bishir Maigora,Jami’in hulda da jama’a na (1) Idris K Bala, Jami’in hulda da jama’a na(2) Abba Soja Daudawa, Sakataren kudi Abba Kwai.
Bugu da kari an kaddamar da shugabannin kungiyar a matakin mazabu goma inda Ahmed Zakari ya kasance shugaban kungiyar mazabar Mairuwa da kuma Alhasan Danlami shugaban kungiyar na karamar hukumar.
Ya ce kungiyar tana da magoya baya da suka kai 5000 za kuma ta yi aiki tukuru don ganin dan takarar gwamnan Jihar Katsina na jami’yyar APC, Dakta Dikko Umar Radda ya lashe zaben gwamnan jihar Katsina.
Ya bada tabbatar da cewa duk kuma takarar da aka fito, za a lashe a karkashin jam’iyyar ba ta fadi ba,a karamar hukumar Faskari tun daga sama har kasa APC duk jam’iyyar ce za a zaba.
Manyan jagororin jam’iyyar APC a karamar hukumar Faskari dabandaban sun yi bayanai na jinjinawa kan irin kokarin da jagororin jam’iyyar APC na karamar hukumar Faskari suke yi.
Musamman ma babban jagora Kwamishinan muhalli na Jihar Katsina Honorabul Hamza Sulaiman Wamban Faskari, da sauran mukarrabansa, da suka hada da mataimakin Shugaban majalisar Jihar Katsina mai Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki da shugaban karamar hukumar Faskari Honorabul Bala Ado, tare da daukacin kansilolin karamar hukumar kokarin da suke na ciyar da jam’iyyar APC a karamar hukumar.