Kamfanin Sufurin jirgin sama na Azman, a ranar Alhamis ya bayyana cewa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya NCAA ta dakatar da ayyukansa ne saboda lasisinsa na Air Operator (AOC) ya kare.
Shugaban kamfanin Azman Air, Abdulmunaf Sarina, wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da LEADERSHIP, ya ce za a sabunta AOC na kamfanin.
A cewarsa, kamfanin jirgin zai koma aiki saboda za a sabunta AOC din a ranar Alhamis.
“Lasisin mu ya kare, amma yau (Alhamis) za mu sabunta shi,” in ji shi a sakon da ya aike wa LEADERSHIP.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a safiyar ranar Alhamis ne NCAA ta dakatar da kamfanin na Azman Air saboda gazawarsa na sabunta AOC dinsa.
Dakatarwar na zuwa ne ‘yan watanni bayan NCAA ta dakatar da kamfanin Dana Air saboda fuskantar wasu matsaloli da suka faru akai-akai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp