An nada mamba kuma jigo a jam’iyyar PDP sannan Sanatan da ke wakiltar mazabar Enugu ta Gabas, Chimaroke Nnamani a cikin kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 da ke karatowa.
Hakan na kunshe cikin jerin sunayen da aka fitar a daren ranar Juma’a inda aka nemi sunan mataimain shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo sama da kasa cikin jerin kwamitin yakin zaben na Tinubu aka rasa, inda aka rawaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya umarci mataimakin nasa da ya maida hankali kawai wajen gudanar da mulki.
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Ministocin BRICS
- Dakarun Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya
Kazalika, jam’iyyar ta ki sanya sunan tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Yakubu Dogara, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; tsohon ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da dan-gani-kashenin Tinubu, Adebayo Shittu, wadda ya jagoranci manyan kungiyoyin goyon bayan Tinunu, ‘Asiwaju Tinubu-Shettima Coalition for Good Governance’ dukka babu sunayensu.
A wata sanarwar da jami’in watsa labarai na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Festus Keyamo (SAN) ya fitar, ya ce an cire sunan Osianbajo da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha daga cikin kwamitin yakin zaben ne sakamakon umarnin da shugaba Buhari ya bayar na cewa su maida hankali wajen gudanar da harkokin mulkin Nijeriya a halin yanzu.
Jerin kwamitin yakin zaben mai mutum 422 da sakataren kwamitin yakin zaben, Hon. James Faleke ya fitar, kuma an gano cewa wasu jerin fitattun jigogin jam’iyyar babu sunayensu a ciki.
Kazalika, shugaba Muhammadu Buhari shine shugaban kwamitin yakin zaben, Bola Ahmed Tinubu kuma shine mataimakin shugaba na kwamitin yakin zaben APC, yayin da kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya kasance darakta-janar yakin neman zabe na Tinubu.
Tsohon shugaban jam’iyyar, Kwamared Adams Oshiomhole shine aka ayyana a matsayin mataimakin darakta-janar nay akin zaben a sashin ayyuka, sanna akwai sunayen gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisu, jakadu, da wasu jiga-jigai cikin kwamitin yakin zaben na Tinubu.
A sanarwar ta Keyamo, ya ce sabanin yadda wasu rahotonni ke yawo na cewa an cire sunayen wasu na kusa-kusan Buhari cikin kwamitin yakin zaben da kokarin nuna cewa akwai Baraka a jam’iyyar, ya ce sam ba haka zancen yake ba, illa dai ya nuna cewa Buhari ne ya umarci Osinbajo da Boss da su maida hankali wajen gudanar da mulki.
“A matsayin jam’iyyar da ta san meye take yi da gwamnatin da ta san meye take yi, ba zai yiyu a kwashe dukkanun manyan jami’an gwamnati a ce su bar ayyukansu su shiga kwamitin yakin zabe ba. APC ita ce ke da ikon jan ragamar Nijeriya har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023, don haka akwai bukatar wasu su fi maida hankali wajen gudanar da harkokin mulki ba zallar yakin zabe ba.”