Kungiyar Malaman Jami’o’i ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi, kamar yadda Leadership Hausa ta tabbatar.
Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, wakilinmu ya tattaro cewa an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
- Tsarin Gwamnatin Sin Na Ba Da Jiyya Ga Dukkanin Mazauna Kauyuka
- Takaddama: Mawakin Buhari, Rarara Ya Fara Yi Wa Ganduje Gugar-Zana
Da yake zantawa da wakilinmu, wata majiya mai karfi a hukumar NEC ta ce, “Eh, an dakatar da shi”.
Da aka nemi karin bayani, majiyar ta ce, “Shugaban zai fitar da wata sanarwa a hukumance da safe”.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa kungiyar malaman ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022.
Yajin aikin ya haifar da koma baya ga harkar ilimi, da kuma tada jijiyar wuya a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin.