Gwamnatin Jihar Jigawa ta hada kai da Kasar Netherland domin dakile matsalar ambaliyar ruwa da ta addabi wasu sassan jihar.
Gwamna Mohammed Badaru Abubakar ne, ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin kwararru kan yadda za a shawo kan ambaliyar ruwa daga Kasar Netherlands a ofishinsa da ke Dutse.
- Wakilan Amurka Da Rasha Sun Tattauna Kan Batun Yakin Ukraine
- Za A Iya Fuskantar Yunwa Sakamakon Ambaliyar Ruwa – Sarkin Zazzau
Ya yi bayanin cewa gwamnatin Jihar Jigawa ta hada gwiwa da kwararrun domin samar da mafita mai dorewa ga matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar jihar a duk shekara.
A cewarsa, kasar Netherlands tana da tarihin gudanarwa da sarrafa ambaliyar ruwa sama da shekaru 300.
“Muna bukatar mafita don kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi da ake yi duk shekara da kuma ganin yadda za a canza ruwa zuwa fa’idar tattalin arzikin Jihar,” in ji Badaru.
Gwamna Badaru ya ce “Za a shawo kan ambaliyar kuma a ajiye ruwan domin a yi amfani da shi wajen noman rani.”
Leadership Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitoci guda biyu masu domin dakile illolin ambaliyar ruwa a jihar.
Sama da mutane 133 ne suka rasa rayukansu da asarar dukiya da ta kai Naira tiriliyan 1.5 a ambaliyar ruwa a bana a fadin jihar.