An haramta wa mai harama da Hajji ko Umura ya sadu da iyalinsa. Haka nan sauran abubuwan da za su iya janyo saduwar.
Haramun ne aikata duk wani sabon Allah ga mai harama (wannan ma ko babu harama ya haramta ballantana kuma an yi haramar).
An hana wa mai harama da Hajji ko Umura yin jayayya ko gardama ta banza ko rikici da wani. Koda shedan ya zuga wani ya ya tinkaro ka da wadannan abubuwa kar ka biye ma sa, ka yi hakuri.
Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya yi Hajji bai sadu da iyalinsa ba, bai yi batsa ko fasikanci ko sabon Allah ba, zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” Ma’ana babu zunubi a tare da shi.
Wasu Malamai sun yi sharhin cewa za a iya yin tattaunawa ta ilimi. Amma a wannan zamanin jayayya ta fi yawa, don haka zai fi kyau a yi ta-ka-tsan-tsan wurin yin tattaunawar ma.
Wata rana Shehu Ibrahim Kaulakha ya je Hajji sai ya shiga shagon wani mai sayar da littafai ya sayi littafi ya biya, sai mai shagon ya ce sam ba a biya shi kudin ba. Wanda ya raka Shehu shagon zai bude baki ya yi magana Shehun ya dakatar da shi. Sai ya sake dauko kudin ya baiwa mai shagon.
Sun fito shagon sun kama hanya sai mai shagon nan ya ga kudin, ya biyo su Shehu a guje ya ce ya ga wurin da ya ajiye wancan kudin na farko, sai ya tambayi Shehu cewa, me ya sa tunda ya san ya biya shi bai dage kan haka ba, Shehu ya ce ma sa Allah ya hana jayayya a Aikin Hajji. Don haka a kiyaye sosai.
Haramun ne ga mai harama namiji ya daura duk wani abu dinkakke, sai dai hirami kawai. Amma idan bai samu hirami ba, babu laifi ya daura wando kamar yadda Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito daga cikin hudubar da Annabi (SAW) ya yi a ranar Arfa.
Idan mai harama bai samu silafas ba, zai iya sanya takalmi sawu-ciki, amma ya yanke shi zuwa karkashin idon sawunsa kamar yadda ake wa khuffi.
Wannan duk an haramta ne ga namiji. Amma ita mace babu abin da ya haramta mata illa sanya turare, nikabi da safar hannu, kamar yadda Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW).
Haka nan kar ta sanya kayan da aka yi musu rini da turare, amma idan rini ne kawai babu turare shikenan. Bayan wannan, za ta iya sanya duk abin da take so.
Akwai Malaman da suka yi shisshigin cewa mace za ta iya sanya nikabi, amma kuma ya kamata a fahimci cewa idan Shari’a ta zo da abu, namu bi ne kawai. Don wandanda suke ganin za a iya rufe fuskar saboda kishin matan ai ba su kai Annabi (SAW) kishi ba. Ya kamata a yi hattara.
Haramun ne mai harama da Hajji ya yi aure ko ya daura wa wani ko wakilta wani. Idan kuma aka yi, to ya baci.
Ba a yarda mai harama ya yanke farce ko cire gashinsa a ko wace gaba ba (askewa ko ragewa). Amma an yi sauki idan farcen ya karye, babu laifi a cire gutsiren da ya rage shi kadai. Idan kuma yana cutuwa da gashin wani wuri a jikinsa, zai iya cirewa amma sai ya ba da hadaya.
Game da gashin gira, sauran Maz’habobi sun ce za a iya cirewa babu komai, amma Imam Malik ya ce shi ma sai an ba da hadaya.
Haramun ne sanya turare walau ga namiji ko mace. Za a iya sanyawa ne kafin a yi harama. Hatta Alhajin da ya mutu a wurin Aikin Hajji ba a sanya ma sa turare bayan an ma sa wanka.
Annabi (SAW) ya ce “Idan Alhaji ya mutu, kar a rufe ma sa kai, kar a sanya ma sa turare, zai tashi ranar kiyama a matsayin Alhaji.”
Babu laifi idan turaren da ake shafa wa Ka’aba ya shafi mayafin Alhaji, ba sai ya wanke ba. Amma dai kar mutum ya je da gangar da nufin shafawa.
Haramun ne ga mai harama ya yi farauta a kan kasa ko ya nuna wa wani abin farautar ko ya taimaka wa mai yi, amma ya halasta ya yi a cikin ruwa kuma ya ci.
Hukuncin wanda ya aikata daya daga cikin abubuwan nan da aka hana bisa uzuri (ban da saduwa da iyali) shi ne, ya ba da hadayar akuya. Idan ba shi da ita sai ya ciyar da miskinai shida. Ko wane miskini a bashi rabin sa’i. Ko kuma ya yi azumin kwana uku.
Wanda ya yanke gashinsa guda uku ko abin da ya fi haka, zai yi fidiya da akuya.
Imamus Shafi’i ya ruwaito cewa idan mutum ya tsige gashi daya, hukuncinsa shi ne ya ba da abinci cikin tafi daya (Muddan Nabiy daya), idan ya tsige biyu; zai ba da biyu, idan yawansu ya kai uku; sai ya ba da jini (akuya).
Haka nan ba a so Alhaji ya shafa mai (mai kamshi ko mara kamshi) lokacin da yake cikin harami. Idan ya shafa, hukuncin ba da jini (akuya) ya hau kansa. Imam Abu Hanifa ya ce a ko wace gaba aka shafa; wannan hukuncin ya hau kan mutum, ba a kebe wasu gabobi da aka amince a shafa musu ba. Amma a wurin Imam Shafi’i, idan an shafa wa kai ko gemu ne hukuncin jinin yake aukuwa. Koda yake shi ya yi sauki a kan shafa mai mara kamshi, sai dai shi ma ban da kai da gemu.
Hukuncin Saduwa Da Iyali A Hajji
Babu abin da yake bata Aikin Hajji kada’an da ba za a iya gyarawa da kaffara ba sai Saduwa da iyali.
Sayyidina Aliyu (RA) da Sayyidina Umar (RA) da Sayyidina Abu Huraira (RA) sun ba da fatawar cewa duk wanda ya sadu da iyalinsa bayan ya yi harama da Aikin Hajji, Hajjinsa ya baci. Kuma wajibi ne ya ci gaba da aikin har ya kammala. Sannan zai ba da rakumi ko saniya, ya kuma dawo wata shekarar ya sake yin wani Hajjin.
Abul Abbasid Dabari, ya ce idan mai Aikin Hajji ya sadu da iyalinsa kafin halastawa karama, Hajjinsa ya baci. Ma’anar halastawa karama ita ce daga lokacin da mutum ya yi harama zuwa tsayuwar Arfa har zuwa Jifa na ranar Sallah da hadaya da aski ko saisaye, sai bai samu ya tafi Makka ya yi Dawafi ba, to an halasta ma sa abubuwan da aka haramta ma sa lokacin da ya yi harama (irin su sanya kayan gida, aski, shafa turare, shafa mai da sauran su) amma ban da saduwa da iyali.
Ita ma matar da aka sadu da ita alhali ta yi harama da Hajji, Hajjin nata ya lalace, kamar yadda wasu malamai suka bayyana. Ita ma za ta karasa sauran ayyukan da suka rage, kuma za ta ba da jini (rakumi ko saniya). Koda yake akwai Malaman da suka ce idan ita da mijin suka ba da daya (rakumin ko saniya) ya isar musu, ba sai ita matar ta bayar da nata daban ba.
Idan za su dawo wata shekarar su rama Hajjin, shari’a ta ce a raba tsakaninsu domin rigakafin sake aukuwar hakan.
Idan wanda ya sadu da iyalinsa ya kasa ba da rakumi; sai ya ba da saniya, idan ya kasa; sai ya ba da awaki, idan ya kasa; sai a yi ma sa kimar kudin rakumin ko lissafin adadin abinci ya bayar. Ko wane Miskini zai ba shi Muddan Nabiy daya. Idan kuma bai samu ba, sai ya yi azumi na adadin yawan Muddan Nabiy da zai bayar.
Amma su a wurin Ma’abota Zahiri, idan mutum ya sadu da iyalinsa Hajjinsa ya baci sai dai zai ba da akuya ne kawai.
A wani hukuncin kuma, idan mutum ya sadu da iyalinsa bayan halastawa karama, to babu komai a kansa, kamar yadda galibin Malamai suka tafi a kai. Sai dai wani sashen na Malamai sun ce mutum zai rama kuma hadaya ta wajaba a kansa, kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bin Umar (RA), Hasanul Basri, Ibrahimun Naka’i. Abdullahi bin Abbas (RA) ya karfafa batun ba da rakumi kamar yadda shi ma Ikrimah ya fada.
Imamu Malik da Imamu Shafi’i su kuma sun yi sauki inda suka ce a ba da akuya.
Idan Alhaji ya yi mafarki ya sadu da iyalinsa har maniyyi ya fito, ko ya dinga tunanin saduwa har maziyyi ya fito ma sa ko kuma saboda kallo na sha’awa ya fitar, Hajjinsa bai baci ba kuma babu komai a kansa.
Saboda yin hakan ba saduwa ba ce. Amma kuma duk wanda ya shafa mace da nufin sha’awa ko ya sumbace ta da sha’awa; zai ba da akuya, walau ya fitar da maniyyi ko maziyyi ko bai fitar ba. An ruwaito wannan ma daga Abdullahi bin Abbas (RA).
Yana da matukar kyau kowa ya kiyaye wadannan abubuwa domin a samu Hajjin da ya kubuta daga dukkan aibi, ma’ana Hajjan Mabrur.‎ Allah ya ba da iko.