Jami’an ‘yansandan Nijeriya a Jihar Adamawa sun kama wani matashi dan shekara 32 mai suna Joseph Nwakibe bisa zargin aikata damfara.
‘Yansandan sun ce sun kama wanda ake zargin dauke da katin cirar kudi (ATM) daban-daban har guda 10.
- Kurar Sauya Fasalin Kudi: ‘Mahaukatan’ Sayen-sayen Da Masu Boye Kudi Ke Yi
- Shirin Nijeriya Na Yaki Da Talauci A Duniya
Rundunar ‘yansandan, a cikin wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar, Suleiman Nguroje, ya sanya wa hannu, ta ce jami’an ‘yansanda sun yi ta sa ido a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, inda suka cafke matashin.
Rundunar ‘yansandan ta ce Joseph, dan asalin karamar hukumar Nnewi ta Kudu a Jihar Anambra da ke zaune a garin Markudi na Jihar Benuwe, an kama shi ne a wajen cirar kudi na bankin First Bank da ke Yola, babban birnin Jihar Adamawa.
Rundunar ‘yasandan ta kuma bayyana cewa abokinsa Obinna Ajima ne ya gayyace shi zuwa Yola domin gudanar da aikin damfara na hadin gwiwa.
SP Nguroje, ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin tare da abokansa sun tafi da katunan ATM da yawa da suka daina aiki don nuna cewa su abokan hulda ne.
Suna bin layin kamar kwastomomi kuma suna ba da taimako ga duk wanda suka ga yana da matsala wajen wajen cirar kudi wanda daga nan ne suka dauke lambobin katin cirar kudi na mutane.