Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta sanar a yau Jumma’a cewa, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Indonesiya Joko Widodo ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai isa tsibirin Bali na kasar Indonesiya, don halartar taron kolin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 karo na 17, wanda zai gudana daga ranar 14 zuwa 17 ga watan da muke ciki.
Haka kuma, bisa gayyatar da firaministan kasar Thailand Prayuth Chan-ocha ya yi, shugaba Xi zai isa birnin Bangkok na kasar, tsakanin ranar 17 zuwa 19 ga wata, don halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Asiya da yankin tekun Pasific a fannin tattalin arziki ko APEC karo na 29, wanda zai gudana a kasar Thailand, kana zai gudanar da ziyarar aiki a kasar.
Ana sa ran shugaba Xi zai gana da takwarorinsa na wasu kasashe, yayin ziyararsa ta wannan karo, wadanda suka hada da Emmanuel Macron na Faransa, da shugaba Joe Biden na kasar Amurka, da Macky Sall na kasar Senegal, da dai sauransu.
A yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa a wannan rana, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana fatan kasar Sin, game da halartar ayyukan da shugaba Xi Jinping zai gudanar.
Game da taron kolin G20 na tsibirin Bali, Zhao ya ce, wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin zai halarci taron koli na bangarori da dama, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20.
Ya ce a halin yanzu, duniya na fuskantar kalubale a fannin samun ci gaba, kuma a matsayinsa na babban dandalin hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa, ya kamata kungiyar G20 ta karfafa hadin kai, tare da daidaita manufofin tattalin arziki, da yin kokari tare, don neman dauwamamman ci gaban tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.
Game da kwarya-kwaryar taron kolin na APEC, Zhao ya ce, APEC wani muhimmin dandali ne na hadin gwiwar tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasifik. Kuma shugaba Xi Jinping zai gabatar da muhimmin jawabi a gun taron, inda zai yi cikakken bayani kan muhimman manufofin kasar Sin, game da zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da tekun Pasifik, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin yanki da na duniya baki daya.
Zhao ya kara da cewa, “Muna sa ran dukkan bangarorin za su amince da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Asiya da tekun Pacific, tare da sanya sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin yankin, har ma da dukkanin duniya.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)