Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo bai halarci taron gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC, a Jihar Filato ba.
Taron, a cewar Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu, shi ne wanda aka mika tutar jam’iyyar ga dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda ya ce ya ba Osinbajo damar zama abokin takarar Buhari.
- Mambobin ASUU A Bauchi Sun Yi Zanga-zanga Kan Bukatunsu
- Nan Kusa Rikicin Atiku Da Gwamnonin PDP ‘Yan G5 Zai Zama Tarihi – Saraki
A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke halartar taron, jaridar Leadership Hausa, ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bai halarci taron ba.
Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya sa mataimakin shugaban kasar bai halarci taron yakin neman zaben da aka gudanar a Jos, babban birnin jihar Filato ba.
Wasu da dama a makonnin da suka gabata sun nuna damuwarsu kan dalilin da ya sa Osinbajo baya cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Buhari.
Ana rade-radin cewa da gangan Osinbajo ya nisanta kansa daga kwamitin yakin neman zaben Tinubu saboda wasu dalilai da shi ya sani.
Ana dai cewa har yanzu Osinbajo na bakin ciki kan rashin nasarar da ya yi a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da Tinubu ya yi.