• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Samar Da Cikakken Tsaro Ga Hukumar Zabe Ta INEC

by Leadership Hausa
3 years ago
Tsaro

Daga dukkan alamu akwai wani shiri na musamman daga wasu makiya tsarin dimokuradiyya na ganin sun yi wa kokarin Hukumar Zabe INEC na gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa zagon kasa.

Hare-haren ban takaidi da ake kaiwa ofishoshin hukumar a sassan kasar a ‘yan wattanin nan alamu ne da ke nuni da hakan.

A makon da ya gabata ne, wasu da ba a kai ga gane ko su wanene ba su ka kai hari tare da kone ofishin INEC a Jihar Ogun bayan sun fi karfin masu gadin ofishin. Rahottanin sun nuna cewa, an lalata ginin ofishin da wasu kayayyakin aiki da suka hada da akwatunan zabe 904, gurbin kebewa don kada kuri’a guda 29, amsa kuwa 30 da jakankunan zabe 57 da kuma teburan zaman jami’an zabe sama da 8, sauran kayan da aka lalata sun hada da katin zabe na dindin 65,699.

  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kama Wani Guda Daya
  • Gudummawar Kamfanonin Fasahar Sadarwar Kasar Sin Ga Kara Dunkulewar Duniya

Hakanan kuma Kwamishinan zabe na Jihar Osun, Mutiu Agboke, ya sanar da cewa, an banka wa ofishin hukumar da ke karamar hukumar Ede ta Kudu wuta, idan kuma za a iya tunawa ‘yan daba sun kona ofishin INEC da ke karamar hukumar Igbo-Eze a Jihar Inugu da ke yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Hukumar ta sanar da cewa, duk da cewa babu wani mutujm da ya rasa ransa amma an lalata akwatunan zabe 748, wurin kebewa don kada kuri’a guda 240, kayayyakin amfani na ofis duk kuwa da kokarin da ofishin kashe gobara na Jihar Inugu daga garin Nsukka yayi don shawo kan gobarar.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Bayani ya kuma nuna cewa a watan Afrilu na wannan shekarar, INEC ta sanar da cewa, ta yi asarar na’urar ‘card reader’ da ya fi guda 99,836 a hare-haren da aka kai mata har guda 42 a ofsihoshinta da wadanda aka kai wa ma’aikatanta a cikin shekara uku, haka kuma a wasu bayanai da INEC ta bayar ta sanar da cewa, ya zuwa watan Mayu na shekarar 2021, an kai mata hare-hare da suka kai 41 a jihohi 14 a fadin tayayyar kasar nan a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021. A shekarar 2019 kawai, hukumar zaben ta fuskanci hare- hare 9 a jihohi 4, a shekarar 2020 kuma ta fuskanci hare-hare 21 a jihohi 9, haka kuma a shekarar 2021 an bayar da rahoton hari 11 a jihohi 7 na tarayyar kasar nan. A rahoton, sun ta bayyana cewa, hare-haren ya kunshi kone-kone da lalata mata kayayyaki.

Yadda kone-konen ke kara karuwa a kan ofishoshin INEC da kuma mugun nufin wadanda ke kai hare-haren ya fara tayar da hankulan al’ummar kasa har ana tunanin hare-haren za su iya shafar sahihandin babbar zaben shekarar 2023. Ra’ayin wannan jaridar shi ne lallai wadannan hare-haren a bayyane yake cewa da gangan ne ake yin su da nufin tsorata wasu al’umma daga kada kuri’a tun ma kafin a fara harkar zaben.

A nasu bangaren, kasashen Birtaniya da Amurka sun nuna damuwarsu ga hare-haren da ake kai wa ofisoshin hukumar da yadda ake lalata kayayyanin aiki su a fadin tarayyar kasar nan, sun kuma yi gargadin cewa, lallai wannan babbar barazana de ga zabukkan 2023 kuma barazana de ga ita kanta harkar dimokradiyya da kanta.

Duk da hukumar bata huta ba wajen ganin ta gudanar da sahihin zabe ta hanyar samar da hanyar aika da sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa da na’urar BIBAS amma wasu ‘yan siyasa sun dukufa wajen yin zagon kasa ga wannan shiri na hukumar zaben ta hanyar kai hare-hare a kan kayan aikin hukumar INEC musamman a wuraren da suke ganin basu da magoya baya masu yawa, inda suke abokan hamayyar su ne ke da mafi yawan al’ummar da ke a yankin.

Wani karin abin damuwa a nan kuma shi ne mastalar tsaron da ta fuskanta a wasu sassan kasar nan. Muna daukar wadannan matsalolin guda biyu a matsayin abubuwan da za su iya shafar yadda za a gudanar da sahihin zabe cikin kwandiyar hankalin a 2023.

Tuni rahoto ya nuna cewa, akwai wasu al’umma fiye da 686 da suke karkashin ikon ‘yanbindga. Idan za a iya tunawa a watan Yuni na wananan shekarar ne, kungiyar ‘yanta’adda ta Ansaru ta haramta harkokin siyasa a masarautar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Haka kuma matsalar tsaro a yankin Arewandin Nijeriya ya tarwatsa miliyoyin al’umma daga gidajensu na gado. Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an staro su tabbatar da samar da tsaro daga nan zuwa ranar 31 ga watan Disamba. Muna fatan Allah ya basu nasarar samar da cikakiyar zaman lafiya a Nijeriya.

Tabbas mun ji dadin yadda aka samar da karin matakan tsaro a ofishoshin INEC a sassan Nijeriya don kare aukuwar karin hare-haren da ake yi.

Bayani ya nuna cewa, an samar da jami’an ‘yansanda, sojoji, DSS da jami’an hukumar kashe gobara don kare ofishoshin na INEC a sassan Nijeriya. Bugu da kari Babban Sufeton ‘Yansanda, Usman Alkali, ya umarci Kwamishinonin ‘yansanda su samar da shirin tsaro na musamman don kare ofishoshin INEC a fadin tarayyar kasar nan.

A kan wadannan matsololin muke kira ga jami’an tsaro dasu tabbatar da kamawa tare da hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin kai hari ofishoshin hukumar zabe na INEC. Tabbas masu kai hare-haren nan ba aljannu ba ne.

Yakamata a tona masu asiri a kuma hukunta su. Suna ci gaba da kai hare-haren ne don babu wanda aka kama aka kuma hukunta. A ra’ayinmu in har aka kai ga kama ‘yansiyasar da ke daukar nauyin masu kai hare-haren tare da hukunta su, to zai taimaka wajen rage hare-haren da ake yi.

A matsayinmu na gidan jarida mun tsaya a kan bukatar gudanar da sahihin zabe a shekarar 2023 da wasu shekarun masu zuwa nan gaba, fatanmu ita de a tabbatar da ra’ayin al’umma de ke yin galaba a zabubbukan da za a gudanar. A ra’ayinmmu kuma daya daga cikin hanyoyin da za a iya dimma wannan burin shi ne tabbatar da cikakken tsaro ga ma’aikata da dukkan kayayyakin zabe da INEC ta tanada.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima
Manyan Labarai

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
Buhari Ya Kafa Tarihi Bayan Shekara 63

Buhari Ya Kafa Tarihi Bayan Shekara 63

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.