ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa – MDD

by Sadiq
3 years ago
Arewa

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a Nijeriya, ya bayyana cewa har yanzu ba a shawo kan matsalar jin kai a yankin Arewa maso Gabas ba, yayin da mata da kananan yara suka rasa muhallansu a shekarar 2022.

A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya a cikin 2023, miliyoyin mutane a Njjeriya za su ci gaba da fuskantar talauci, yayin da da dama kuma za su yi ta fadi tashin neman abinci.

  • An Kaddamar Da Ginin Sabuwar Hedikwatar Kungiyar ECOWAS
  • Tura Mu Aka Yi Mu Sace Sanatan APC- Wasu ‘Yan Bindiga Da Suka Shiga Hannu

Arewa maso gabashin Nijeriya ya kasance daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya, inda akalla mutane sama da miliyan takwas ke bukatar agaji a shekarar 2023.

ADVERTISEMENT

Matsalolin da mata da maza da yara ke fama da su a kowace rana a fadin Jihohin Borno da Adamawa da Yobe har yanzu na karuwa, a cewar rahoton.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ana bukatar kusan Dala biliyan 1.2 domin tallafawa mutane miliyan 5.4 a fadin Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Rahoton ya ci gaba da cewa, a shekarar 2023, mutane miliyan 339 a fadin duniya za su bukaci agajin jin kai, wanda ya karu da kusan kashi 24 cikin dari idan aka kwatanta da bara.

Rahoton ya kara da cewa bukatun jin kai sun karu matuka saboda yakin da ake yi a Kasar Ukraine da kuma tasirin matsalar sauyin yanayi a yankin Gabashin Afirka da yankin Sahel da Pakistan da kuma Nijeriya.

“A yankin Yamma da Tsakiyar Afirka kadai, ana sa ran mutane miliyan 69 za su bukaci agajin jin kai a shekarar 2023, inda ake fargabar cewa Arewa maso Gabashin Nijeriya da Burkina Faso, wadanda ke fama da matsananciyar yunwa, za su iya shiga cikin mummunan yanayi, musamman idan matsalar sauyin yanayi ta tsananta,” in ji Majalisar Dinkin Duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi
Hotuna

HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi

December 20, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yansanda 3 Da Wasu A Sakkwato 

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yansanda 3 Da Wasu A Sakkwato 

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.