Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ta koka kan zargin muzgunawar da jami’an tsaro da Gwamnatin Jihar Zamfara ke wa ‘ya’yanta na daure su a gidajen yari bisa yarfen siyasa.
Shugaban riko na jam’iyyar a jihar Hon. Mukhtar Lugga, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Gusau.
- Abubuwan Lura Guda 6 Game Da Sabbin Dokokin CBN Na Mu’amalar Kudi
- PDP A Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Sadiq Wali Da Abacha
Lugga, ya zargi gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro da kame mambobinsu bisa zarge-zarge marasa tushe bare makama kawai bisa abin da ya misalta kokarin firgitarwa da razanar da mamboninsu
Ya kuma bayyana cewa dan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya na jam’iyyar kuma tsohon ministan yada labarai, Alhaji Ikra Aliyu Bilbis, ya shafe tsawon mako guda a tsare a gidan yari tare da gurfanar da shi gaban kotu kan zargin daukar nauyin ‘yan bangar siyasa wajen lalata allunan tallan jam’iyyar APC a babban birnin jihar.
“Kuma tsauraran sharuddan da kotu ta sanya na belinsa sun saba wa tsarin mulki da rashin adalci na sai ya kawo manyan sakatare wanda ke bakin aiki a yanzu ne kafin a bayar da belin .inistan, wanda ya saba wa hankali da doka wanda ba shi da gwamnati ta yaya zai kawo ma’aikacin gwamnati ya yi belinsa? Shugaban ya tambaya.
Lugga ya kuma koka da yadda aka kama tare da daure tsohon jakadan Kasar Guinea Conarcri, Mai Riga Muhammad a matsayin wanda bai yi laifin komai ba sai don yana jam’iyyar PDP.
“Tsohon jakadan ya kwashe sama da wata guda a gidan yari kuma shari’arsa tana tafiyar hawauniya, kuma har yanzu ana yi mana barazana daga gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawalle tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro na kama duk wanda ya fito fili ya ayyana shi dan jam’iyyar PDP ne a Zamfara.”
Shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro na jihar da kuma babban Sufeton ‘yansanda a kan a taimake su kan halin da jam’iyyar PDP da mutanenta ke ciki na matsi da takurawa.
Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da su sa baki a cikin lamarin domin samun zaman lafiya don a halin yanzu dimokradiyya na fuskantar barazana a Jihar Zamfara.