Sufeto-Janar na ‘yansanda, Usman Baba, ya bayar da umarnin dakatar da Drambi Vandi, dan sandan da ya harbe wata lauya a Legas, Bolanle Raheem.
Mataimakin Sufeton ‘yansandan yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Ajiwe da ke karkashin hedikwatar shiyya ta Ajah na rundunar ‘yansandan Jihar Legas.
- ‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Caji Ofis Da Bam A Anambra
- Ko Gezau Babu Abun Da Ke Firgita Takarata Ta Gwamnan Gombe – Inuwa
Vandi ya harbe Bolanle, wata lauya mai juna biyu bayan ta tsayar da motar ta a ranar Lahadi.
Marigayiyar da ‘yan uwanta na kan hanyarsu ta zuwa gida ne bayan yin siyayyar ranar Kirsimeti.
Wata sanarwa a ranar Laraba ta bakin kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ta ce Sufeton’yansandan na jiran cikakken rahoton faruwar lamarin.
Kakakin ya ce shawarar dakatar da jami’in ya yi daidai da tsarin ladabtarwa na cikin gida na rundunar.
Adejobi ya lura cewa ci gaban zai haifar da yanayi mai dacewa don hanyoyin da suka dace na doka don tabbatar da adalci a cikin shari’ar ba tare da tsangwama ba.
Kakakin ya kara da cewa “Dakatarwar wani tsari ne na ladabtarwa,” in ji shi.
Rundunar ‘yansandan ta bai wa jama’a tabbacin dagewa wajen ganin an yi adalci tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.