Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga ilimi da karfafa matasa a matsayin hanyar sake gina kasar nan idan aka zabe shi a babban zaben 2023.
Kwankwaso, ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake zanta wa da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
- NIS Ta Bankado Sabbin Dabarun Da Masu Safarar Mutane Ke Amfani Da Su A Jihar Bayelsa
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe 14, Sun Yi Garkuwa Da 81 A Sokoto Da Katsina
Ya ce matasa masu hazaka, tare da yin amfani da basirarsu yadda ya kamata, za su taimaka wa muhimman bangarorin gina kasar nan.
Ya kuma yi tir da halin da Nijeriya ke ciki da ya jefa yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta, inda ya yi alkawarin ganin an bai wa yaran ilimi mai inganci tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.
A cewarsa, kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da siyasa da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu, sakamakon rashin ilimi ne kai tsaye wanda ya haifar da fatara da rashin aikin yi a tsakanin matasa masu tada zaune tsaye.
Yayin da yake mika godiyarsa ga magoya bayansa da suka yi masa maraba, tsohon gwamnan Jihar Kano, ya bayyana fatansa na ganin jam’iyyar NNPP ta lashe zaben 2023 mai zuwa.