Kasar Sin ta riga ta kwashe shekaru 3 tana kokarin daukar matakan kandagarkin yaduwar cutar COVID-19, da suka hada da gudanar da gwaji ga mutane, da killace wadanda suka kamu da cutar, da sa ido kan yanayin lafiyar jikin mutanen da ke son yin bulaguro, da dai sauransu. Sai dai a kwanakin baya, gwamnatin kasar ta sanar da daidaita matakan, da sassauta manufar killacewa.
Misali, a yanzu ba a bukatar duba sakamakon gwajin PCR kafin a shiga cikin galibin wurare a kasar. Kana mutanen da suka kamu da cutar COVID-19, wadanda yanayin da suke ciki ba shi da tsanani, za su iya zama a gida yayin da jikinsu ke farfadowa, maimakon killace su a wani wuri na musamman don ba da hidimar jinya. Haka zalika, an soke kayyade zirga-zirga, da manufar dakatar da ayyukan kasuwanci.
- Shugaba Xi Ya Aikewa Shugaba Cyril Ramaphosa Sakon Taya Shi Murnar Sake Zaben Sa A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ANC
- Xinjiang Ta Soki Matsayar Amurka Ta Sanya Wani Kamfanin Fasaha Cikin Jerin Kamfanonin Da Ta Kakabawa Takunkumi
Ban da haka, wata sanarwar da hukumar kula da lafiya ta kasar ta fitar a ranar 26 ga wata, ta ce kasar Sin ta kuma sauyawa cutar suna daga “novel coronavirus pneumonia” wato matakin cutar mai tsanani dake shafar huhu, zuwa “novel coronavirus infection”.
Haka kuma, daga ranar 8 ga watan Junairu na shekarar 2023 dake tafe, kasar Sin za ta sassauta matakanta na yaki da cutar daga rukunin A zuwa rukunin B, bisa dokokin kandagarki da yaki da cutar, tare da cire ta daga jerin cututtukan dake bukatar killacewa, bisa dokokin kiwon lafiya da na killacewa na kasar.
Yanzu haka, an mayar da cutar COVID-19 zuwa rukunin B, amma kuma matakan kandagarki da dakile yaduwarta na karkashin rukunin A.
Sanarwar da kwamitin kula da matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar, na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar, ta ce an riga an dauki dukkan matakan da suka kamata, wadanda za su taimakawa wajen daidaita sassauta matakan, bisa dogaro da yanayin sauyawar cutar da kuma yadda ake tunkararta a kasar.
Sannan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a Talata, 27 ga wata cewa, daga ranar 8 ga watan Junairu, za a soke gwajin cutar COVID-19 ga matafiyan daga ketare.
Sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce ana shawartar masu zuwa kasar Sin daga ketare, su yi gwajin cutar sa’o’i 48 kafin lokacin tafiyarsu. Inda kuma ake shawartar wadanda gwaji ya nuna sun kamu da cutar, su jinkirta tafiyar zuwa lokacin da gwaji zai nuna ba sa dauke da ita.
Haka kuma, babu bukatar matafiya su nemi manhajar tantance yanayin cutar ta Health Code, daga ofisoshin jakadancin kasar Sin.
A cewar sanarwar, za su bayyana yanayin lafiyarsu ne a katin da za su gabatarwa jami’an kwastam. Wadanda kuma yanayin lafiyarsu ke da matsala ko suke dauke da zazzabi, za su yi gwaji a wurin, sannan kuma za a nemi su killace kansu a gida ko su je asibiti, bisa la’akari da yanayin lafiyarsu.
Me ya sa a yanzu kasar Sin ta dauki sabuwar manufar?
Wannan sabuwar manufa ta nuna yadda kasar Sin ta daidaita manufarta, ta neman kawar da cutar COVID-19 gaba daya, wadda ta yi kokarin aiwatar da ita cikin kusan shekaru 3 da suka gabata.
Sai dai me ya sa kasar Sin ta canza manufarta a yanzu? Dalili shi ne, bayan da hukumomin kasar suka kwashe shekaru 3 suna kokarin dakile cutar COVID-19, yanayin da kasar ke ciki ya riga ya sauya sosai, kamar yadda jami’an gwamnati da masana na kasar suka fada.
Da farko dai, COVID-19 nau’in Omicron da ke samun yaduwa a kasar Sin a yanzu, kusan ba ta haddasa alamu masu tsanani, ko da yake tana da saurin yaduwa. Wannan halayya ta cutar ta nuna cewa, ba za ta haifar da babbar illa ga lafiyar jikin galibin al’ummun Sin ba, idan an kwatanta ta da nau’ikan COVID-19 da aka taba gani a baya.
Mista Zhong Nanshan, fitaccen likita ne na kasar Sin, kana kwararre a fannin cututtuka masu alaka da numfashi. A cewarsa, kashi 99% na mutanen da suka harbu da Omicron za su iya warkewa cikin kwanaki 7 zuwa 10. Kana karfin cutar a fannin kashe mutane ya kusan yin daidai da na mura.
A birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, wani sabon karon yaduwar cutar COVID-19 da ya abku a kwanan baya, ya sa mutane fiye da dubu 160 kamuwa da cutar, amma bai haddasa mutuwa ba, in ji Tang Xiaoping, shugaban jami’ar koyon ilimin likitanci ta Guangzhou. A cewarsa, fiye da kashi 90% na mutanen da suka kamu da cutar ba su nuna wata alamar rashin jin dadi ba, ko kuma sun nuna wasu alamu, amma ba su yi tsanani ba.
Na biyu shi ne, fiye da kaso 90 na al’ummar kasar sun karbi allurar rigakafin cutar COVID-19, kamar yadda alkaluma daga hukumar kasar suka nuna. Kana kashi 91% na mutanen kasar da shekarunsu suka haura 60, wadanda suka fi fuskantar hadari idan sun kamu da COVID-19, an riga an yi musu allurar rigakafi, bisa alkaluman da aka gabatar a ranar 28 ga watan Nuwamba. Kana har zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin na kokarin neman ganin karin tsoffin mutane su karbi allurar rigakafi.
Me ya sa Sin ba ta dauki sabuwar manufar tun a baya ba?
Me ya sa kasar Sin ta jira har kusan shekaru 3, kafin ta gyara manufarta ta kandagarkin cutar COVID-19, yayin da kasashe da dama suka zabi dabarar “zama tare da kwayoyin cutar COVID-19” tun tuni?
Hakika kasar Sin na ta kokarin daidaita manufar dakile cutar COVID-19, don tabbatar da ingancinta, ta yadda tasirinta ba zai shafi mutane da yawa ba, bisa tantance yanayin da ake ciki a kai a kai. Sa’an nan a yanzu haka ne aka samu sharadi na daukar sabuwar manufar kandagarkin cuta, bayan namijin kokarin da kasar ta yi wajen dakile cutar cikin shekaru 3 da suka wuce, a cewar hukumomi masu kula da aikin lafiya.
A lokacin da aka gano kwayoyin cutar COVID-19 a birnin Wuhan na kasar Sin a karshen shekarar 2019, cutar ta fi karfin kisa. Sai dai gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar daukar mataki na sanya daukacin mazauna birnin zama a gidajensu ba tare da jinkiri ba. Bayan watanni 3, kasar ta samu shawo kan yanayin cutar a birnin Wuhan, da hana ta bazuwa zuwa sauran wuraren kasar.
Daga bisani, karkashin manufar kokarin kawar da cutar COVID a kai a kai, kasar Sin ta samu nasarar shawo kan barkewar annobar COVID a wurare fiye da 100 na kasar, ta yadda ta iya kare lafiyar jikin al’ummarta ta biliyan 1.4.
A sa’i daya, gwamnatin kasar ta sa kaimi ga aikin yi wa jama’a allurar riga kafin cutar, ganin yadda aka samu shaidu kan amfanin allurar ta fuskatar magance mutuwa, da yanayin cutar mai tsanani.
Tabbas, kwayoyin cutar COVID-19 na dinga sauya salonsu, daga nau’in Alpha, zuwa Beta, da Delta. Sa’an nan yanzu ta sauya zuwa Omicron, yayin da yawan mutanen da suka rasa rayuka sakamakon cutar ke kara raguwa. Amma wannan canzawar salo ta faru ne sannu a hankali, cikin wasu shekaru 3 da suka wuce.
A lokaci guda, mutane fiye da miliyan 6.62 sun rasa rayuka a duniyarmu, sakamakon harbuwa da annobar. Yayin da yawan mutanen kasashe daban daban da suka taba kamuwa da cutar ya zarce mililiyan 642, bisa alkaluman da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar.
A kasar Amurka, wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma kasar dake da ci gaba a fannin aikin jinya, an samu mutane fiye da miliyan 1.09 da suka rasa rayukansu sakamakon cutar COVID, yayin da kimanin mutane miliyan 100 na kasar suka harbu da cutar, bisa alkaluman da kasar ita kanta ta gabatar.
Idan har a kasar Sin, wadda yawan al’ummarta ya ninka na kasar Amurka har fiye da sau 4, kana ingancin tsare-tsaren aikin jinya bai kai na kasar Amurka ba tukuna, aka dauki manufar kandagarkin COVID iri daya da na kasar Amurka, to, hakan zai iya haddasa rasa rayukan miliyoyin mutane a kasar.
Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID mafi kankanta
Har zuwa yanzu, idan an kwatanta yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID, da yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar, a manyan kasashe na duniya, za a ga jimillar kasar Sin ta fi kankanta.
A cewar Zhong Nanshan, a ranar 28 ga watan Nuwamban shekarar bana, yawan mutanen da suka kamu da COVID bisa yawan al’ummar Sin shi ne kashi 1 cikin kashi 374 na matsayin duniya, kana kashi 1 cikin kashi 1348 na kasar Amurka. Yayin da yawan mutuwa na kasar Sin shi ne kashi 1 cikin kashi 232 na matsakaicin adadin na duniya.
A sa’i daya kuma, matsakaicin tsawon ran mutane a kasar Sin ya karu daga shekaru 77.4 a shekarar 2019, zuwa 77.93 a shekarar 2020, kana ya kai shekaru 78.2 a shekarar 2021, bisa alkaluman da gwamnatin kasar ta gabatar.
Kana dalilin da ya sa aka samu wannan ci gaba a kasar Sin, shi ne hukumar kasar na mai da kare rai da lafiyar jama’a gaban komai, yayin da take tsara manufar dakile cutar COVID-19.
Ko wadanne ayyuka kasar Sin ta yi a kokarinta na dakile COVID-19 cikin shekaru 3 da suka gabata?
A cikin wadannan shekaru 3 ke nan, kasar Sin ta yi iyakacin kokarin kare rayuka da lafiyar jikin jama’arta, tare da samar da dimbin fasahohi masu daraja a wannan fanni ga duniya.
Ban da wannan kuma, kokarinta na dakile yaduwar cutar ya sa an samu lokacin da ake bukata, don gabatar da dabarun kimiyya da fasaha, na tantancewa, da shawo kan kwayoyin cutar.
Rayukan jama’a sun fi muhimmanci
Yayin da take tsara manufofi, gwamnatin kasar Sin har kullum tana kallon rayukan jama’a da lafiyar jikinsu da matukar muhimmanci, wadanda suka kasance a gaban komai.
A lokacin da aka gano barkewar cutar COVID-19 a birnin Wuhan na kasar, gwamnati ta yanke shawarar killace birnin gaba daya, inda aka dakatar da zirga-zirgar motoci da jiragen kasa da na sama, gami da na ruwa. Sa’an nan bayan watanni 3, kasar ta samu nasarar kawar da cutar a birnin Wuhan, da hana bazuwarta zuwa sauran sassan kasar.
Bisa kididdigar da hukumomin kasar Sin suka yi, a tsakanin manyan kasashe na duniya, kasar Sin ce ke da mafi kankantar yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19, da ma yawan mutane da suka rasa rayuka sakamakon cutar, bisa yawan al’ummar kasar.
Gudanar da aiki bisa tushen kimiyya da fasaha
Kasar Sin tana gudanar da ayyukan dakile cutar COVID-19 ne bisa tushen kimiyya da fasaha, da kokarin tabbatar da kimar matakan da aka dauka. Kasar tana kuma daidaita manufarta ta fuskar dakile cutar a kai a kai, ta la’akari da karin ilimin da aka samu dangane da cutar, bisa binciken da ake yi a kanta.
Gwamnatin kasar Sin ta riga ta sabunta tsare-tsaren tinkarar annobar har sau 9, bisa yadda kwayoyin cutar ke ta sauya salo, daga nau’in Alpha, zuwa na Beta, da Delta, gami da na Omicron na yanzu.
Fiye da kashi 90% na al’ummar Sin sun karbi allurar rigakafin cutar COVID-19, inda aka yi musu allura har sau 3. Kuma har zuwa yanzu, gwamnati na ci gaba da kokarin lallashin tsoffin mutane don su karbi allurar rigakafin, yayin da sabon nau’in rigakafi na fesa ruwan magani cikin kofar hanci domin a shaka, shi ma aka fara yin amfani da shi a kasar.
Ban da haka, kasar ta samar da allurar rigakafi wajen biliyan 2.2 ga sauran kasashen da suke da bukata.
Kokarin rage hasarar da za a samu
A sa’i daya kuma, kasar Sin na kokarin neman samun daidaituwa tsakanin matakai na kandagarkin yaduwar cutar COVID-19, da aiki na raya tattalin arzikin kasar, ta yadda za a kare rayuka da lafiyar jikin mutanen kasar, gami da rage hasarar da za a iya samu sakamakon matakan kandagarkin cutar da aka dauka.
Kasar Sin tana cikin kasashe na jerin farko da suka samu karuwar tattalin arziki a shekarar 2020, inda matsakaicin karuwar tattalin arzikinta ya kai kashi 5.1%, a shekarar 2020 da ta 2021.
Kana yayin da kasar ke kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19, tana kuma ci gaba da gudanar da wasu manyan ayyukan kimiyya da fasaha ba tare da samun katsewa ba, wadanda suka hada da aiki na tara bayanan alkaluma daga yankunan gabashin kasar, sa’an nan an gudanar da aikin kirga a kansu, a yankunan yammacinta, gami da aikin gina cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar. Duk wadannan manyan ayyuka na ci gaba da gudana ne bisa shirin da aka tsara a baya.
Haka zalika, gwamnatin kasar Sin ta yafe wa kamfanoni masu zaman kansu haraji da sauran kudin da ya kamata su biya, da yawansu ya kai fiye da kudin Sin Yuan triliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 143, don neman tabbatar da farfadowar wadannan kamfanoni cikin sauri, da karuwar tattalin arzikin kasar.
Kokarin da kasar Sin ta yi a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19, ya shafi dukkan bangarorin da suka hada da aikin kiwon lafiya, da tattalin arziki, da yadda hukumomin kasar ke gudanar da ayyuka masu alaka da mulki, da nazarin kimiyya da fasaha, da dai sauransu. Sa’an nan bayan da kasar ta kwashe shekaru 3 tana yin hakan, a karshe dai ta samu damar saukaka dabarun kandagarkin cuta, a wannan lokacin da muke ciki.
(Bello Wang)