Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta tura karin dakarunta domin tabbatar da tsaro yayin ziyarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai jihar.
Rundunar ta kuma umarci jami’ai da su nuna kwarewa sosai da kuma mutunta hakkin dan adam.
- Alakar Gwarzon Dan Kwallo Pele Da Afirka
- Chadi Ta Dakile Yunkurin Juyin Mulki Tare Da Kame Wadanda Suka Kitsa
Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Yola.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa Buhari zai je jihar ne a ranar Litinin mai zuwa domin kaddamar da yakin neman zaben ‘yar takarar gwamnan jihar, Sanata Aishatu Binani.
Ana sa ran jami’an tsaro za su sa ido a boye tare da yin sintiri.
“Tawagar ta ba da tabbacin hadin gwiwa da kyakkyawar alakar aiki tsakanin dukkan hukumomin tsaro wadanda za a yi aikin tare da su.
“Sannan kuma hukumar’yansanda ta kuduri aniyar yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki ‘yan kishin kasa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar kafin da lokacin ziyarar shugaban kasa da kuma bayan ziyarar.
Nguroje ya ci gaba da cewa, kwamishinan ya kuma ba da umarnin hana zirga-zirgar ababen hawa musamman wadanda ke fitowa daga hanyar Sangere-Numan zuwa garin Yola zuwa mahadar FGGC ta hanyar tashar motocin Jambutu zuwa mahadar Doubeli.
Ya ce wadanda ke fitowa daga garin Yola zuwa filin jirgin sama, an shawarce su da su bi hanyar rukunin gidaje 80 ta hanyar kwamishinoni zuwa zagayen Mubi.
“Rundunar ta na nadamar rashin jin dadi da ta haifar, ta yi kira ga jama’a da su gudanar da ayyukansu tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba su,” in ji shi.