A bayyana yake cewa a halin yanzu Nijeriya na fadi tashi a neman samar da ci gaba a bangarori da dama, tun daga bunkasar tattalin arzki zuwa samar da ingantaciyar rayuywa ga al’umma, ana fuskantar matsaloli da dama da suke kawo wa Nijeriya cikas a kokarinta na neman ci gaba.
Amma tabbas akwai hanyoyin da suka kamata Nijeriya ta bi wajen samun mafita tare da maganin wadannan matsalolin, sun kuma hada da sanya ido da kuma karfafa mahukunta na jihohi don su tabbatar da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana, hakanan a tabbatar da matakin kananan hukumomi na yin aiki yadda ya kamata, musamman ganin sune a kusa da al’umma.
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki Ba
- Me Sin Ta Kawo wa Duniya Cikin Shekaru 3 Da Ta Shafe Tana Kokarin Tinkarar Cutar COVID-19
Daya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a Nijeriya shi ne na rashin kyakkyawar gwamnati a matakin jihohi, jihohi da dama sun zama dandalin cin hanci da rashawa suna gudanar da ayyukansu a kudundune wanda hakan yana shafar kokarin cigaba a fadin kasar nan. In har ana son Nijeriya ta samu ci gaban da ya kamata dole a sa ido a yadda Jihohi suke gudanar da ayyukansu tare da hukunta jami’an da aka tabbatar sun aikata ba daidai ba a dukkan matakan tafiyar da harkokin jihar.
Daya daga cikin hanyoyin tabbatar da ganin haka shi ne karfarfawa jami’an gwamnatin gwiwa jihohi su gudanar da harkokin mulki a bayyane ba tare da boye-boye ba. Za kuma a iya cimma wannan manufar ta hanyar yin amfani da dokar bayyana ayyukan gwamnati a kuma ba al’umma damar sanin dukkan yadda gwamnatin ke gudanar da ayyukanta don kowa ya sani.
Haka nan za a iya cimma wannan maufan ne ta hanyar amfani da fasahar bibiyar yadda ake aiwatar da kasafin kudi, ta haka ne al’umma za su iya sani tare da bibiyar yadda ake kashe kudadensu, suna kuma iya kama duk wani jami’in gwamnatin da ya kauce hanya ko kuma ya yi halin bera.
Yana da matukar muhimmanci a karfafa al’umma su shigo don su sani tare da bibiyar yadda ake sarrafa dukiyar gwamnatocinsu. Wannan kuma za a cimma masa ne ta hanyar samar da kungiyoyin matasa ‘yan fafutuka a tarukan da suke yi na kungiyoyin za su rinka fadakar da al’umma halin da ake ciki don suna da hakkin sanin yadda ake sarrafa dukiyoyinsu.
In aka ba al’umma damar sanya baki a kan yadda ake gudanar da harkokin gwamnatin jihohinsu, hakan zai tabbatar da gwamnati na gudaar da ayyukan da suka shafi rayuwar al’ummar ne wanda hakan kuma yana matukar muhimmanci a fagen bunkasar rayuwar al’umma a bangaren tattalin arziki dana zamantakewar kasar baki daya.
Wasu hanyoyin da za a karfafa samar da ci gaba a matakin jihohin Nijeriya sun kuma hada da zuba jari a bangaren gine-gine na da matukar muhimmanci a hanyar tabbatar da ci gaba kowanne iri saboda shine ginshikin tabbatar da bunkasar tattalin arziki. Zuba jari wajen gina abubuwa kamar su hanyoyi gadoji tashashoshin jiragen ruwa ta haka kuma za a samar da ayyukan yi ga dimbin matasanmu wanda hakan zai kai ga bunkasar tattalin arzik zai kuma kai ga daga darajar rayuwar al’ummar kasa.
Amma kuma yana da matukar muhimmanci a tabbatar da an yi ingantattun ayyuka wadanda za su amfanar da al’umma, musamman ganin a lokutta da dama ana samun sakaci da rashin sanin yakamata wajen gudanar da ayyukan ci gaba a jihohin kasar nan.
Ta hanyar tabbatar da ana gudanar da ingantattun ayyuka a matakin jihohi, Nijeriya za ta samu tabbacin jihohi suna bayar da gudummawarsu wajen bunkasar kasar gaba daya.
Akwai kuma wasu hanyaoyin na daban inda Nijeriya za ta bayar da karfi in har ana son a tabbatar da ci gaba mai dorewa a matakin jihohin kasar nan. Misali ana iya karfafa bangaren ilimi ta yadda za a fito da hanyoyin da za a bunkasa ilijkin al’umma musamman samar da cikakkne horas da matasa sana’o’in dogaro da kai don da ilimi ne kasashe ke samun bunkasar tattalin arzik a fadin duniya.
Za kuma a iya mayar da hankali a kan karfafrawa tare da bayar da tallafin da ya kamata ga kananan masa’ana’antu musamman wadanda Suke bayar da gudummawar tabbatar da ci gaban tattalin arziki.
A bayyane lamarin yake cewa, a kwai gaggarumin aiki a gaban Nijeriya a kokrinta na wanzar da ci gaba a matakin jihohi.
Amma in har aka samar da yanayin da za a rike sanya ido akan yadda jihohin ke gudanar da ayyukansu to lallai Nijeriya ta dauki matakin samar da ci gaban da ake bukata a kasar baki daya a yanzu da kuma nan gaba.
A ra’ayinmu, wannan ne lokacin da ya dace na aiwatar da wannan matakan musamman ganin muna dunfarar babban zaben kasa.
Abin takaci a nan shi ne yawancin ‘yan Nijeriya sun mayar da hankalinsu ne a kan abin da ke faruwa a matakin gwamnatin tarayya sun manta da abin da ke faruwa a matakin gwamnatocin Jihohi da sauran matakan gwamnati.
Muna iya cewa, kyakyawar gwamnati ta mutu a matakin jihohi da kanana hukumomi. Kwanakin baya ne hukumar kididdiga ta kasa ta bayar da rahotannin tsananin talaucin da ake fama da shi a Nijeriya, in da aka bayyana cewa, kashi 63 na ‘yan Nijeriya na fama da talauci, ko kuma a ce ‘yan Nijeriya Miliyan 133 ke fama da talauci, wannan yana nuna sakaci da rashin iya aiki na gwamnati. Amma kuma abin takaicin shi ne al’umma sun fi dora alhaki a kan gwamnatin tarayya kuma in aka lura lafin duk da hannu sauran matakan gwamnati.
Nijeriya za ta iya samun cikakken ci gaba ne in aka tabbatar da wakilci daidai a dukkan matakan gwamnati, shugaban kasab ba zai iya yin komai da komai ba dukk da irin fatansa na alhairi.
A kan haka muke kira ga masu zabe sun zabi ‘yan siyasa masu mutunci da za su iya yin aikin da ya kamatra a dukka matakai musamman a matakin jihohi. Ta haka ne Nijeriya za ta samu bunkasa zuwa matakin da dukkan mu muke mafarki kuma muke bukata.