A makon da ya gabata, wata amarya mai suna Khadija Abdullahi ta rasa ido ana tsaka da bakinta a Jihar Kano.
Da yake zantawa da LEADERSHIP Hausa, angon Khajita mai suna Malam Mustapha Bala bayyana cewa ya samu labarin amaryasa Khadija ana tsaka da biki na nuna murna, sai wasu matasa suka yi dukan kan mai uwa da wabi da na nufin tarwatsa taron, wanda aka zargi cewa ‘yan bijilanti ne suka afka musu. A sanadiyyar haka ne aka bige idanun amarya.
- Buni Ya Zabtare Kaso 35 Na Farashin Shaguna A Sabbin Kasuwannin Yobe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Tarwatsa Sansaninsu A Kaduna
Ya ce a yanzu haka tana kwance a daya daga cikin manyan asibitocin Jihar Kano, domin kula da lafiyarta. Ya nemi hukumomi da sauran kungiyoyin kare hakkin Bil’adama su kawo musu dauki na ganin an kwato musu hakkisu na yin sanadin mayar da ranar farin ciki zuwa akasin haka.
Amarya Khadija ta ce suna cikin biki ne kawai aka afka musu wanda ba ta fargaba kawai sai ganin kanta a asibiti.
Shi dai angon, ya bayyana cewa soyayya na nan daram da amaryarsa, kuma ana sa ran ma idon zai warke da yardar Allah, inda a yanzu haka an kama wasu mutum biyu da ake zargi da wannan aika-aikata.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, wani malamin addini, Malam Abdullahi Muazu, ya bayyana wannan lamari a matsayin abun damuwa da bakin ciki, inda kuma ya nemi a yi bincike domin gano masu wannan ta’asa da nufin hukuntasu kamar yadda doka ta yi tanada.