Kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, (PDPCC) ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da hukumar yaki da safaran miyagun kwayoyi (NDLEA) da su gaggauta cafke dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan zargin da ake masa na safaran miyagun kwayoyi da yin ruf da ciki da dukiyar jiha.
PDP din ta ce a wani taron manema labarai da suka yi a ranar Lahadi a Abuja, bayan an kama Tinubu din to a hanzarta gurfanar da shi a gaban kuliya kan wadannan zarge-zargen.
Kakakin kwamitin yakin zaben, Mista Daniel Bwala ya bukaci NDLEA ta nemi cikakken bayani daga wajen Tinubu don ya fayyace bayanai kan dalilan da suka janyo har hukumomi a kasar Amurka suka kwace masa Dala 460,000.
Bwala, kazalika ya yi tir da wata kungiyar da ya ce Tinubu kafa, da ya ce kamar kungiyar ce ta mayakan sa-kai, sai ya nemi hukumomin tsaro da su cafke da gurfanar da duk wani da ya kasance cikin kungiyar mai suna ‘Jagaban Army’.
Sun Yi zargin cewa an kafa kungiyar ne kawai domin kawo yamutsi da firgici gabanin da yayin zabuka.
Ya kara da cewa mambobin jam’iyyar adawa da dama su na fuskantar kalubale na barazana kashi-kashi gabanin zaben 2023.
Wani ma daga cikin masu magana da kwamitin yakin zaben PDP, Phrank Shaibu, shi ma ya zargi Tinubu har yanzu na nan tsundum cikin zargin harkarlar kwayoyi.
Kazalika kwamitin ya zargi Tinubu Wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne da yin sama da fadi da dukiyar jihar a lokacin da yake matsayin gwamna.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne bayanai suka karade cewa wata kotu a Amurka ta kwace wasu dalolin Amurka daga asusun Tinubu a yankin arewacin Illinois kan zargin alaka da fataucin kwayoyi.
Sai dai kuma takardun ba su bada wasu bayanai ko tabbatar da cewa anyi wa Tinubu shari’a ba, ko kuma yana da alaka da wata kungiyar fataucin kwayoyi.
Takardun sun kuma nuna cewa an yi wannan shari’a ne shekaru 30 da suka gabata.
A cewar bayanan, wannan yanayi ne ya tursasa wa Tinubu sadaukar da kudaden da yawansu ya kai dala 460,000 a daya daga cikin asusun bankunansa 10.