Jiya Litinin hadaddiyar kungiyar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta gabatar da ma’aunin sayen kaya PMI ta fuskar aikin kera kaya na watan Janairun da ya gabata, inda ma’aunin da ya rika raguwa a cikin watanni 7 a jere, yanzu ya farfado, har ma da karuwa bisa na watan Disamban bara.
Wasu masana sun bayyana cewa, masana’antun samar da kaya na kasar Sin sun ba da gudunmawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya.
Mataimakiyar shugaban sashen kula da harkokin Amurka da Turai a cibiyar tuntubar kasa da kasa ta fuskar tattalin arziki ta kasar Sin, Zhang Monan ta nuna cewa, ma’aunin PMI na aikin kera kaya ya nuna cewa, a watan Janairu, masana’antun samar da kaya na Sin sun samu karuwa bisa na watan Disamban bara saboda farfadowar tattalin arzikin kasar mai inganci, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen hana raguwar tattalin arzikin duniya.
A cewarta, ma’aunin PMI ta fuskar aikin kera kaya na duniya na kasa da 50% har yanzu, abin da ya nuna cewa, ana bukatar kara karfin hana raguwar tattalin arzikin duniya. A sa’i daya kuma, ana iya ganin cewa, matsalar cutar COVID-19 na ci gaba da kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kana karancin bukatu na ci gaba da zama matsalar da kasashen duniya ke fuskanta. Haka zalika, kasashe da dama suna kokarin hana hauhawar farashin kaya tare da ingiza bunkasuwar tattalin arziki.
Darektan cibiyar nazarin tattalin arzikin shiyya-shiyya na ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin Zhang Jianping ya jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su amince da bambancin dake akwai tsakaninsu, kana su hada kansu, da kuma kara hadin kai a fannin cinikayya da tattalin arziki, don maido da bunkasuwar tattalin arzikin duniya bisa hanyar da ta dace. (Amina Xu)