Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta yi alkawarin ci gaba da yaki da cutar daji ko da bayan ta bar mulki.
Dakta Zainab dai, wacce kuma ita ce shugabar gidauniyar Medicaid Cancer Foundation ta bayyana hakan a Birnin kebbi a wani taron tattaunawa da ‘yan jarida a wani bangare na kokarin ganin ta samu nasarar gudanar da aikinta daga shekarar 2015 zuwa yau.
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”
- Matsalar Tsaro Ta Haifar Da Koma-baya A Jihohin Arewa —Masari
A cewarta, ” cutar daji za ta ci gaba da ta’azzara. Za ta ci gaba da karuwa kuma ana bukatar karin Ma’aikatan da za su gudanar da aiki don magance matsalar cutar daji.
”Har ila yau, akwai rashin daidaituwa a cikin ayyukan da ake bukata da kuma isassun kudi. Ya kamata a ga ciwon daji a matsayin matsala da za a baiwa muhimmanci da gaggawa.
“Zan ci gaba da gudanar da ayyukana na tuntubar jama’a don gudanar da yekuwar da wayar da kan jama’a da ake bukata ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jaha da na kasa baki daya.”
Haka Zalika, Dakta Zainab Bagudu ta ci gaba da cewa, gwamnati da masu ruwa da tsaki a shirye suke su dauki matakin gaggawa domin dakile yaduwar cutar.
Ta yi alkawarin yin aiki tare da gwamnati, kungiyoyi farar hulla da duk masu ruwa da tsaki don kara yawan kudade don yaki da cutar daji, tare da samar da matakan rigakafi.
”Wannan babbar matsala ce a Nijeriya kasancewar kasar ba ta yin abin da ya dace idan aka yi la’akari da yawan al’ummar kasar.
Har ilayau, “Hadin gwiwa mai karfi yana da matukar mahimmanci ta wannan hanyar kamar yadda tsarin tuntubar kasa shima yana da mahimmanci.
Ta ce “Jihar Kebbi ta yi abubuwa da yawa. Muna da tsarin kula da cutar kansa da kuma asusun kansa na marasa galihu.
“Haka kuma akwai tsarin inshorar lafiya musamman a matakin PHC kuma dole ne mu kara himma wajen samar da karin ayyuka,” in ji Dakta Zainab Shinkafi Bagudu.
Ta yi godiya ga maigidanta Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da duk masu ruwa da tsaki bisa yadda aka amince da dokar kare hakkin yara da mata a jihar Kebbi.
Sun hada da dokar BAPP, dokar kare hakkin yara da kuma dokar GBB, inda suka ce matakin da gwamnatin jihar karkashin jagorancin maigidanta Abubakar Atiku Bagudu ta yi abin yabawa ne matuka.
Daga nan ta jaddada bukatar jama’a musamman wadanda aka zalunta da iyayen wadanda aka yi wa fyaden su rika fadin albarkacin bakinsu tare da kai rahoton irin wannan lamari.
”Ya kamata jama’a su dauki matakin da ya dace kuma su samu hujjojin da suka dace. Yakamata kuma a dage da wayar da kan jama’a,” in ji ta.