Sanata Ahmad Rufai Sani Hanga, wanda ya tsayawa takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa sanar da sunan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya samu nasara a jam’iyyar NNPP, akwai a lamar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta raina kotu, domin kuwa tun da farko a wannan danbarwa ta taso ya kai kara a karo na farko ya samu nassara, sannan haka a kotun daukaka kara nan ma ya yi nasara, wandea kotu ta ba da umarni a sa sunansa, amma ba a saba.
Ya ce yana ganin wannan raini ne ga kotu da INEC ta yi ko kuma aiki ne ya yi mata yawa, amma wannan ba wani abun damuwa ba ne za a warware matsar, a cewar sanata Ahmad Rufai Sani Hanga, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a shalkwatar yada manufarsa ta jam’iyyar NNPP da ke Kano a ranar Talatar da ta gabata.
Haka kuma ya ce akwai irin wadanan matsalolin da dama a NIjeriya, wanda dan takara daban kuma wanda INEC ta sanar da sunansa daban, domin yanzu haka shugaban majalisar dattawa ta kasa, Sanata Ahmad Lawan ba sunansa aka sanar ba, sunan Machina ne aka sanar a matsayin wanda ya ci wannan zabe.
A cewarsa, haka kuma ta faru ga ‘yan majalisar tarayya da na jihohi mai takara daban wanda za a sanar da sunansa daban, saboda haka babu wani abu da zai ba su tsoro.