Dakarun sojin “Operation Whirl Punch’’, da runduna ta musamman ta bataliya ta 167 ta sojojin Nijeriya sun fatattaki ‘yan bindiga a wani kazamin artabu da suka yi a Jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kaduna.
- Ana Goyon Bayan Bukatar Argentina Game Da Ikon Mallakar Tsibiran Falkland
- An Ceto Mutum 46 Da Dukiyar Miliyan 95 Daga Gobara Cikin Wata Daya A Kano
Aruwan ya ce sojojin da suka yi sintiri mai dogon zango zuwa yankin Tukurua a karamar hukumar Chikun ta jihar, sun yi artabu tare da fatattakar masu laifin, inda suka kashe daya, yayin da wasu suka gudu.
“Sojojin a yayin aikin sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da maza tara da mata biyar.
“An kai wadanda abin ya shafa zuwa wani wuri mai tsaro don tantance su kafin a sake sada su da iyalansu,” in ji shi.
Aruwan ya kara da cewa sojojin sun lalata sansanoni da dama a yakin.
“An gano babura biyu yayin aikin,” in ji shi.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-Rufai, ya ji dadin irin nasarorin da sojojin suka samu, ya kuma yaba wa jagorancin Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, Babban Kwamandan Runduna ta 1 da kuma Kwamandan Rundunar ‘Operation Whirlx Punch’’.
El-Rufai ya kuma yaba da bajintar sojojin yayin da aka kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su da ransu, kuma ba tare da sun ji rauni ba.