An bayyana jihohi bakwai a matsayin wuraren da za a iya samun tashe-tashen hankula gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar ranar Asabar.
Biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun siyasa a jihohin bakwai kafin zaben, tsoro ya kama mazauna jihohin.
- An Fitar Da Tsarin Yin Kwaskwarima Na JKS Da Hukumomin Gwamnati
- EFCC Ta Gurfanar Da Farfesa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N1.4bn
Jama’a a jihohin dai sun ce sun shiga cikin fargaba ganin yadda tashe-tashen hankula ke barkewa tsakanin magoya bayan manyan ‘yan takara da jam’iyyun siyasa, musamman daidai lokacin da ake ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jihohin dai kamar yadda rahotanni da nazari suka nuna sun hada da Kaduna da Zamfara da Legas da Kano da Gombe da Ribas da kuma Bauchi. Masu ruwa da tsaki dai na yin kiraye-kirayen ga hukumomin tsaro da su karfafa jami’an tsaro a jihohin gabanin zaben.
Kano
A Kano mazauna jihar sun ce suna fargabar sake ganin irin abin da ya faru a wasu kananan hukumomi a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, da kuma tashe-tashen hankula da suka barke a lokaci da kuma bayan zaben gwamnan jihar na 2019.
Tsoron dai ya kara ta’azzara sakamakon zarge-zargen da ake yi na shirin tayar da fitina daga manyan jam’iyyun siyasa a jihar.
Rundunar ‘yansandan jihar ta kuma tabbatar da samun bayanan sirri na tsaro cewa wasu ‘yan siyasa da ba su ji dadi ba sun kammala shirin shigo da ‘yan daba cikin jihar domin kawo cikas ga zaben.
Wani bangare na mazauna jihar sun tuno da tashe-tashen hankula da aka ruwaito a lokacin yakin neman zabe, da kuma rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyu biyu wato APC da NNPP kwana guda gabanin zaben shugaban kasa a birnin Kano.
Sun ce kone-kone da kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Takai da Tudunwada a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, tuni suka yi nuni ga abin da zai faru a lokacin zaben gwamna.
Legas
Wata jihar da ke kan iya fadawa rikici ita ce Legas. Ana zaman dar-dar a fadin jihar gabanin zaben gwamnan da za a yi ranar Asabar, yayin da jama’a da dama ke cewa suna fargabar yiwuwar tashin hankali, inda ake taho-mu-gama a tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da na jam’iyyar adawa ta LP da PDP.
Kayen da jam’iyyar APC ta sha a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu ya tayar da tarzoma, yayin da jam’iyya mai mulki ke fafutukar ganin ta ci gaba da rike jihar da ta kwashe sama da shekaru 20 tana mulki.
Hankali ya kara tashi a ranar Asabar lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan dan takarar gwamna na jam’iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Bibour a Epe.
Rundunar ‘yansandan Legas ta ce tana aiwatar da dabarun yaki da miyagun laifuffuka don magance tashe-tashen hankula a wasu yankunan da ake yi wa kallon fagen yakin siyasa a jihar biyo bayan wasu sakonnin barazana da aka rika yadawa a shafukan sada zumunta.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Idowu Owohunwa, ya umurci dukkanin kwamandojin yanki da manyan jami’an ‘yansanda da su kai ziyara zuwa rumfunan zabe daban-daban a yankinsu, su kuma kirga rumfunan zabe, sannan su lura da wasu wuraren da za su iya zama barazanar tsaro a yankunansu a lokacin zabe da kuma bayan zabe.
Zamfara
Mazauna Jihar Zamfara dai sun bayyana fargabar tashin hankali gabanin zaben duk da cewa ‘yan takaran na cin karensu babu babbaka kan hare-hare da magoya bayansu ke kaiwa.
Manyan ‘yan takara biyu sun hada da Gwamna Bello Mohammed Matawalle, mai neman a sake zabarsa karo na biyu a jam’iyyar APC, da kuma Alhaji Dauda Lawal Dare, dan takarar gwamna na PDP.
Tun bayan fara yakin neman zabe, ake kai hare-hare kan kowane magoya bayan ‘yan takarar da ofisoshi, da motocin yakin neman zabe da allunan tallace-tallace a cikin jihar.
‘Yan adawa a jihar sun zargi hukumar yaki da ‘yan daba ta jihar da tursasa su, zargin da hukumar ta musanta.
A jajibirin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dakta Dauda Lawal Dare, ya yi zargin yunkurin kashe shi bayan wani hari da jami’an hukumar yaki da ‘yan daba ta jihar suka kai wa ayarin motocin matarsa.
Ya ce, ayarin motocin na matarsa na dawowa ne daga wani taron jam’iyya a Gusau, babban birnin jihar, sai jami’an hukumar gwamnati suka tare shi tare da kai musu farmaki.
Ana kuma fargabar yiwuwar tashe-tashen hankula saboda an ce masu kada kuri’a sun kasa jefa kuri’unsu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, sakamakon barazanar da ‘yan ta’adda suka yi musu na sace su.
Bauchi
A Jihar Bauchi kuwa, ana zaman dar-dar a siyasance wanda ya haifar da tashin hankali tsakanin magoya bayan gwamna mai ci, Bala Mohammed na jam’iyyar PDP da dan takarar babbar jam’iyyar adawa a jihar ta APC, Air Marshal Sadikue Baba Abubakar (rtd).
A cikin watan da ya gabata, jam’iyyun PDP da APC sun yi arangama da juna kan rikicin da ya yi sanadin kashe mutane uku tare da raunata dimbin magoya bayan a lokacin yakin neman zabe.
Wannan al’amari dai ya kara firgita a zukatan da dama daga cikin mazauna jihar, inda suka ce watakila rayuwarsu ba za ta kasance cikin kwanciyar hankali ba a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar.
Tsoron nasu kuma ya ta’allaka ne kan yadda duk ‘yan takarar gwamna na kan gaba a Bauchi na gudanar da yakin neman zabensu tare da ‘yan baranda da ke yin kamfen a matsayin mafarauta na cikin gida da ke baje kolin makamai a lokacin gangamin wanda ke tsorata ‘yan adawa.
Sakwatto
A Jihar Sakwato dai al’ummar gari na fargaban kan zaben gwamna da ke tafe a jihar, saboda tsokanar da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa ke yi.
Dangantakar a tsakanin siyasar jihar dai ya yi tsami ne biyo bayan kalaman batanci da zargi da kuma tofin Allah tsine da aka yi a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa zaben ya yi tashe-tashen hankula, inda aka soke sakamakon zabe sama da rumfuna 400, wanda hakan ya sa INEC ta kasa bayyana sunayen wadanda suka lashe zaben ‘yan majalisun tarayya a zuwa yanzu.
‘Yan takara da jam’iyyunsu sun yi amfani da ‘yan bangar siyasa wajen kawo cikas a zaben da aka gudanar a rumfunan zabe, inda suka fahimci cewa sun sha kaye saboda ka’idojin da hukumar INEC wanda ya bayar da damar soke zabe a wuraren da rikici ya barke.
An kuma bayar da rahoton cewa ‘yan daba sun tarwatsa masu kada kuri’a tare da lalata katunan zabe da akwatunan zabe.
Hakan dai ya biyo bayan yadda mazauna jihar ke cewa suna fargabar fitowa filin zabe domin kada kuri’a a zaben na ranar Asabar.
Gombe
Mazauna Jihar Gombe sun nuna damuwa kan barazanar tashe-tashen hankula da ‘yan daba na siyasa da ake gani a wasu sassan jihar.
Kafin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, akalla mutane biyar ne suka jikkata bayan wasu da ake zargin ‘yan daba sun kai hari gidan wani jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Salisu Abdul’aziz.
Abdul’aziz dai ya kasance dan jam’iyyar APC kafin ya koma PDP. Ya kira taron mata da matasa ne a gidansa da ke unguwar Jekadafari a cikin birnin Gombe a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka mamaye taron tare da tarwatsa mutane.
Yadda Ake Kawar Da Rikicin Zabe – Kwararre
Wani manazarcin harkokin siyasa kuma malami a Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Kamilu Sani Fage, ya ce tashe-tashen hankula sun fi yin kamari a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha, saboda sun fi kusanci da mutane kuma ‘yan siyasan sun fi sanin hanyoyin cin zabe.
Dangane da hanyoyin da za a bi don dakile rikici kuwa, Fage ya ce babban abin da ya kamata a yi shi ne, ‘yan siyasa su yi taka-tsan-tsan da furucinsu da ayyukansu saboda su na da ‘yan daba da suke bai wa kudade domin tayar da zaune-tsaye.
“Ya kamata suna rike mukamansu da ya rataya a wuyan kamar yadda dokar kasa ta tanada, sannan su sani idan babu zaman lafiya babu yadda za a yi su iya gudanar da shugabanci.
“Har ila yau, su ma shugabanin zaben su dunga dauki lamarin da muhimmanci, duk inda aka samu tashin hankali, a binciki irin wadannan da kyau, kuma duk wanda aka samu da laifi a hukunta shi kamar yadda dokar kasa ta tanada,” in ji shi.
A nata bangaren, kungiyar sa ido kan harkokin mulki (TMG) ta ce ana bukatar karin haske da kuma sanya takunkumin da ya dace don dakile tashe-tashen hankulan zabe gabanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi na ranar Asabar.
Shugaban kungiyar TMG, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce duk zabukan da suka yi nasara suna da inganci ta yadda hukumar zabe ta gudanar da shi tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki.
“Wannan shi ne babban dalilin da ya sa dukkanin jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin zaman lafiya guda biyu wajen gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.
“Wadannan yarjejeniyoyin zaman lafiya manyan mutane ne a kasar nan suka jagoranta da ya samu halartar dukkan masu ruwa da tsaki, kamar hukumomin tsaro, kungiyoyin fararen huda, masu saka ido na cikin gida da na kasashen waje da kuma kafafen yada labarai,” in ji shi.
Ya ce dole ne gwamnati da duk masu ruwa da tsaki su tabbatar an yi wa ‘yan siyasa da jam’iyyunsu da magoya bayansu gargadi game da haddasa tashin hankali a lokacin zabe.
Rafsanjani ya ce “Dole ne jami’an tsaro su sanya ido kan dukkan kungiyoyin ‘yan daba wadannan ‘yan siyasa ke dauka don tada tarzoma,” in ji Rafsanjani.