Sakamakon damar da Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Idris Isah Jere ya bayar na kara kwazon ma’aikata ta hanyar bunkasa walwala, hukumar reshen Jihar Ribas ta kafa kwamitin mutum biyar da zai tsara yadda za a inganta walwalar jami’ai ta hanyar gamayya ko alaka da wasu kawayen hukumar.
Kawayen da ake sa ran duba yiwuwar alakar da su sun kunshi masu aiki a bangaren kiwon lafiya, koyar da tsarin gudanar da rayuwa mai inganci ta fuskar samar da abinci da sauran kayan masarufi masu rahusa domin bunkasa walwalar jami’ai manya da kanana da ke aiki a karkashin reshen hukumar na Jihar Ribas.
Sanarwar da sashen hulda da jama’a na NIS reshen jihar ya fitar, ta bayyana cewa domin tabbatar da an yi tsari mai kyau da za a tabbatar da gaskiya da rikon amana saboda jami’an su samu kyakkyawar kulawa, kai-tsaye kwamitin za iyi aiki da masu kawo kayan masarufin da ake bukata.
Reshen hukumar ta NIS na Jihar Ribas ya yaba wa CGI Idris Isah Jere bisa kyakkyawan tsarinsa na shugabanci wanda ya dauki sha’anin bunkasa walwalar jami’ai da matukar muhimmanci.