Kotun sauraren kararrakin zabe a Jihar Kebbi, ta ce ta samu kararraki shida kan zaben ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sakataren kotun, Abdul-Rahaman Muhammad, a wani bincike da wakilin ya gudanar a Birnin Kebbi, ya ce shida daga cikin korafe-korafen sun shafi zaben ‘yan majalisar wakilai, biyu kuma na majalisar dattawa.
- Hukumar Leken Asiri Ta Amurka Ta Sake Tabka Karya Kan Batun “Nord Stream”
- An Yanke Wa Wasu Mutane 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Legas
Haka kuma Abdul-Rahaman ya ce Bala Ibn Na’Allah dan takarar jam’iyyar APC a gundumar Kebbi ta kudu ya shigar da kara mai lamba EPT/KB/SEN/ 01/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben Garba Musa na Jam’iyyar PDP. Ya kara da cewa dan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya, Abubakar Atiku Bagudu shi ma ya shigar da kara mai lamba EPT/BK/SEN/02/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben Muhammad Adamu Aliero na jam’iyyar PDP.
Kazalika Sakataren ya ce dan takarar kujerar Dan majalisar tarayya na jam’iyyar APC, Farfesa Muktar Umar Bunza ne suka shigar da kara mai lamba EPT/KB/HR/04/2023 suna kalubalantar sakamakon zaben mazabar Birnin Kebbi/ Kalgo/Bunza, sai kuma Muhammad Bala Usman na jam’iyyar PDP mai lamba EPT/ KB/ HR/02/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben Yauri/Shanga/Ngaski na majalisar tarayya. Har ilayau Muhammad Umar Jega mai lamba EPT/KB/ HR/ 03/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben Gwandu/Jega/Aliero na tarayya. Sai dai ya ce sauran sun hada da Bello Kabiru na Jam’iyyar PDP mai lamba EPT/KB/HR/01/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben mazabar Suru/Bagudo na majalisar tarayya.
A cewarsa, ‘yan takarar da suka yi korafin suna da kwanaki 21 daga ranar da aka bayyana sakamakon zaben su shigar da kara a gaban kotun. Kotun za ta tsayar da ranar da za a fara sauraren karar bayan kammala musayar takardun kararakin zabe a matakan kotun daga bangarorin biyu.