A yau ne ake sa ran tsohon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump zai je birnin New York daga Florida, gabannin shari’ar da ke jiransa a Manhattan gobe Talata.
Inda za a gabatar masa da duk tuhume-tuhumen da ake yi masa a bayyane.
- Dubi Ga Sabbin Hanyoyin Kutse A Facebook, WhatsApp Da Asusun Ajiyar Banki
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mutum 17 Don Mika Mulki Ga Gwamnati Mai Jiran Gado
Rahotonni sun ce Trump ya yi duk harkokin da ya saba a karshen mako, cikin har da buga wallon sanda (Golf).
Duk da haka, ya tuntubi masu ba shi shawara a kan hanyar da zai bullowa, batun da ya kira makarkashiyar siyasa.
Ana tuhumar tsohon shugaban Amurkan ne da laifin biyan wata mai shirin fina-finan batsa dubban daloli gabannin zaben 2016,a matsayin toshiyar baki.
Ana zargin ya ba ta ne kada ta yi magana a kan zargin da ake yi masa na mu’amala da ita, kafin zaben Amurka na 2016.
To sai dai, a lokuta da dama Trump ya musanta zargin.