ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samar Da Matakan Kauce Wa Yunwa A Nijeriya

by Abdulrazaq Yahuza
3 years ago
Yunwa

Bukukuwan da aka gudanar na ranar abinci na duniya kwanannan sun isa su jawo hankalin gwamnati da al’ummar kasashen duniya a kan matsalar abinci da ake fuskanta a Nijeriya dama wasu sassan duniya, wannan ya zama dole ne musamman ganin matsalar da aka fuskanta sakamakon annobar cutar Korona da kuma matsalar dumamar yanayi a duniya da kuma ambaliyar ruwar da aka fuskanta, ana wannan bikin ne a fadin duniya, ranar da ta yi daidai da ranar da aka kafa kungiyar nan ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNFAO a shekarar 1945, bikin nada matukar muhimmanci don a wannan ranar ce al’ummar duniya ke haduwa don tattaunawa a kan matsalar da ake fuskanta na karancin abinci ko kuma rashin abinci gaba daya a wasu sassan duniya.

Kamar dai yadda shirin samar da abinci a duniya (WFP) ya sanar, shekarar 2022 ya zamar wa al’ummar duniya wata fage na fuskantar matsaloli da suka shafi yanayin samar da abinci wadanda suka hada da rikice-rikice kamar abin da ke faruwa a yakin Rasha da Yukrain da lamarin dumamar yanayi da hauhawar farashin kayan masarufi haka kuma tayar da jijiyar wuya a tsakanin kasashe yana kara haifar da yanayin da noma zai gagara wanda hakan zai ka gai haifar da matsalolin abinci. Wadannan matsalolin sun taimaka wajen haifar da rashin abinci irin wanda ba a taba gani ba a tarihi.

  • Sin Tana Son Ba Da Gudummawar Hikima Don Inganta Zaman Lafiya Da Ci Gaban Yankin Gabas Ta Tsakiya

Ra’ayin wannan jaridar ita ce, an dade ana ta surutu a kan bukatar samar da yanayi da al’umma duniya za su samu damar samun ingantaccen abinci mai gina jiki. A wannan mahangar muke jinjina da godiya da taken bikin na wannan shekarar wanda yake kamar haka, “Tafiya Tare Da Kowa Da Kowa Don Samar Da Ingantaccen Abinci Mai Gina Jiki.”

ADVERTISEMENT

Taken na wannan shekarar ya nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin al’ummar duniya don karfafa tsarin samar da abinci a fadin duniya gaba daya. Wannan ba tare da tantama ba suna cikin manyan matsalolin da al’umma duniya ke fuskanta, cikin su kuma akwai talauci, rashin lafiya da lalacewar muhalli. Don kawo karshen wannan matsalar a fadin duniya a ra’ayinmu dole a samar da wani tsari da zai tafi tare da dukkan al’umma ba tare da nuna banbanci ba domin ai dukkan al’ummar duniya na da muhimmanci wajen samun nasarar wannan aikin.
A kan haka dole Gwamnati, Kamfanoni masu zaman kansu da Malaman jami’o’i da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran daidaikun mutane su yi aiki tare da don samar da yanayin da kowa zai samu abinci cikin kwanciyar hankali ba tare da wani mastala ba.

Abin takaici ne a ra’ayinmu, duk da kokarin da ake yi na samar da ingantacciyar al’umma har yanzu mutane da dama a baya ba a tafiya da su, sun kasa cin gajiyar cigaba da aka samu na kimiyya da fasaha a bangaren tattalin arziki dana zamantakewa. A bayyane lamarin yake, duniya nada abinci da al’umma duniya za su iya ci ba tare da matsala ba amma kuma miliyoyin mutane a fadin duniya na kwana da yunwa wasu kuma basu da ikon samun abinci mai gina jiki.

LABARAI MASU NASABA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Muna kara jaddada cewa, annobar cutar Korona, Dumamar yanayi da mamayar kasar Yukrain da Rasha ta yi ya kawo cikas ga kokarin samar da ingantaccen abinci ga al’umma duniya da kuma shirin kawar da yunwa a fadin duniya.

Kididdiga ya nuna cewa, kashi 75 na mutanen da suke fuskantar matsalar abinci mutane ne da suka dogara da harkar noma a matsayin hanyar samun abincin su, su ne kuma suka fi dandanawa sakamakon da annobar da dan adam ya haifar wa kansa yake kawowa, haka kuma sune suka fi fukantar rikice-rikicen da suka hada da na kabilanci da nuna banbanci a tsakanin maza da mata, wadannan mutanen na matukar bukatar tallafin kudade da kayan aikin noma na zamani don su samu hanyoyin samar da abinci ga al’ummarsu.

A daidai wannan rana ta abinci ta duniya, ya zama dole musamman ganin irin matsalolin da ake fuskanta a sassan duniya duniya su hada hannu don fuskantar matsalar ba tare da nuna banbanci ba, a kan haka dukkan bangarori na rayuwar al’umma suna da gudummawar da yakamata su bayar don samar da abinci ingantacce da zai samar wa al’umma cikakken lafiya.

Bincike ya nuna cewa, a shekafrar 2021 misali, an kiyasta cewa kashi 29.3 na al’ummar duniya kusan mutum Biliyan 2.3 na fuskantar tsanani ko tsakatsakanin matsalar abinci, haka kuma kashi 11.7 na al’umma duniya kusan mutum Biliyan 923.7 na fuskantar kololuwa tsananin matsalar abinci. Haka kuma banbancin da ake samu a tsakanin jinsin mata da maza a kan yadda suke samun abinci yana kara fadada a kullum. A shekarar 2021, kashi 31.9 na mata a duniya na fuskantar matsanancin rashin abinci in aka kwatanta da kashi 27.6 na maza. Rahoton ya kuma bayyana cewa a shekarar 2020, an kiyasta cewa kashi 22 na yara da basu gaza da shekara 5 suna fuskantar matsanancin rashin abinci, yayin da kashi 6.7 na yaran rashin abincin ya yi musu illa wasu kashi 5.7 na yaran kuma suna fuskantar cutar kiba saboda ciye ciye marasa kangado.

Rahoton ya kuma kiyasata cewa, fiye da mutum miliyan 670 a fadin duniya za su fuskanci rashin abinci a cikin shekarar 2030 zuwa 2038, haka lamarin yake a shekarar 2015 a lokacin da aka kaddamar da shirin samar da abinci ga al’ummar duniya nan da shekarar 2030. Mutum fiye da Miliyan 828 aka tabbatar sun fuskanci yunwa a shekarar 2021. Bincike ya kuma nuna cewa daya daga cikin magidanta 8 a duniya na fuskantar cutar kiba a kusan dukkan bangarorin duniya ciki har da kasashe masu tasowa.

Ga Nijeriya kuwa harkokin ‘yan ta’adda yana kara tayar da hankalin al’umma game da shirin samar da abinci sai kuma ga gaggarumar ambaliyar ruwar da ta share filayen noma masu yawa. Ra’ayinmu anan shi ne na bukatar gwamnati ta kawo dauki ga manoman da suka yi asara a sassan Nijeriya. Dole a gaggauta kawar da al’amarin da muke tsoron aukuwarsa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje
Rahotonni

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba
Manyan Labarai

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Next Post
Zaben Jihar Zamfara: Zafin Kaye Ya Sa Gwamna Matawalle Sunbatu A Kan Sojoji

Zaben Jihar Zamfara: Zafin Kaye Ya Sa Gwamna Matawalle Sunbatu A Kan Sojoji

LABARAI MASU NASABA

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

November 15, 2025
Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin

Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin

November 15, 2025
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

November 15, 2025
Yadda Za Ku Gyara Kanku

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.