Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a Kotun Koli a ranar Alhamis yayin da wani Lauya mai fafutukar kare hakkin jama’a, Malcolm Omirhobo, Esq, ya bayyana a gaban alkalai cikin kaya irin na malamai ‘yan gargajiya (matsubbata).
Omirhobo ya bayyana gaban alkalai ne kan hukuncin da kotun ta yanke na ‘yan cin sanya hijabi ga ‘ya’ya mata a makarantun Sakandire dake jihar Legas.
A ranar 17 ga watan Yuni ne kwamitin mutane bakwai na kotun koli ya tabbatar da hakkin dalibai mata musulmi a jihar Legas na sanya hijabi zuwa makaranta ba tare da tsangwama ko nuna wariya ba.
Kwamitin ya shafe hukuncin da wata babbar kotun jihar ta yanke na haramtawa dalibai mata sanya hijabi in suna sanye da kayan Makaranta.
Sai dai Lauya Omirhobo ya isa harabar kotun a yayin da ake zama sanye da jajayen kaya, da wasu kayan gargajiya a wuyansa, da wasu dogayen fuka-fukai guda biyu a gashinsa, sannan kuma ya zana farin alli a idonsa na dama.
Irin wannan shiga da ba a saba gani ba, ta tilasta wa alkalan barin zaman dakin kotun.
Da manema labarai suka nema jin tabakinsa kan ko me yasa yayi Wannan Shigar?
Lauyan ya sanar da ‘yan jarida cewa suturar ta yi daidai da hukuncin Kotun Koli, ta ba da izinin “tufafi na addini” a makarantu, kuma yana da ‘yancin bayyana kansa a matsayin mai bin addinin gargajiya.