A kwanakin baya ne, wasu takardun sirri da dama da ake zargin daga gwamnatin kasar Amurka suka bulla a shafukan sada zumunta.
Wadannan takardu sun nuna cewa, ba wai kawai gwamnatin Amurka tana da hannu a cikin rikicin Rasha da Ukraine ba, har ma tana ci gaba da sanya ido a wasu kasashe ciki har da nata kawayenta. Wannan lamari ya janyo cece-kuce a kasashen duniya.
Wani binciken ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar kan masu amfani da yanar gizo a duniya, ya nuna cewa, kashi 94.6 cikin dari na wadanda aka tattauna da su sun yi Allah wadai da yadda gwamnatin kasar Amurka ke nuna fuska biyu kan batun kiyaye tsaron kasa, suna ganin cewa, aikin ya shaida manufar kama karya ta kasar Amurka. Bisa binciken, kashi 91.3 cikin dari sun yi tsammanin cewa, aikin sa ido na gwamnatin kasar Amurka bai dace ba. Kashi 92.1 cikin dari sun yi tsammanin cewa, aikin ya shaida cewa kasar Amurka ta keta ikon mallakar sauran kasashe da tsaronsu. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp