Wata mace mai shekara 33, mai suna Olaide Adekunle,da ke Ogun, ta sayar da jariririyarta ‘yar wata 18 domin ta biya bashin da ta ce, ya hana ta sukuni.
Matar wadda yanzu haka take hannun ‘yansanda, ta sayar da jariririyar da ta haifa a kan tsabar kudi naira 600,000, ga wasu mutane wadanda har yanzu ba a gano su ba.
- Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?
- Me Ya Sa Karin Kamfanonin Ketare Suka Samu Ra’ayin Bai Daya Kan Zuwa Kasar Sin Don Raya Kansu?
Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya gaya wa manema labarai cewa, an kama matar ce, sakamakon karar da mijinta, mai suna Nureni Rasak ya kai ofishin ‘yansanda da ke Sango.
Mijin ya gaya wa ‘yansanda cewa, matarsa ta je Legas ranar 15 Maris, 2023 da jaririyar, daga nan sai ta dawo gida ba tare da wannan jaririyar ba.
Mista Rasak ya kara da cewa, matarsa ta ki gaya masa inda jaririyar take, duk da barazanar da ya yi yi mata.
Samun wannan labara ke da wuya sai Oyeyemi ya tura wa DPO na Sango CSP Dahiru Saleh, sakon gaggawa wanda shi kuma ya jagoranci mutanensa suka kamo wannan mata.
“Lokacin gudanar da bincike wadda ake zargin ta amsa laifinta cewa ta sayar da jaririyar ga wani mutum a Legas kan naira 600,000,”.
Oyeyemi ta ce “na ranci kudi daga banki, kuma na kasa biya, kuma wanda ya tsaya mini wajen karbar bashin ya takura mini, har yana yi mini barazanar kisa.”
Saboda haka sai na gudu Legas na dinga tallan ruwa.
A lokacin da take tallan ruwan ne ta hadu da wani mutum, wanda ya kai ta wajen wata mata wadda ta sayi jaririyar tata a Legas.
Haka kuma, mukaddashin kwamishinan ‘yansandan jihar DCP Babakura Muhammed, ya bayar da umarnin a mayar da wadda ake zargin zuwa ofishin bincike na CIID domin gudanar da bincike yadda za a gano jariririn.