Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da kakakin majalisar Jihar Ondo, Rt. Hon. Bamidele Oloyeloogun a gaban babbar kotun jihar da ke Akure.
Ana zargin dan majalisar tare da wasu mutum biyu da zambar kudade, zargin da duka mutanen suka musanta.
- Lardunan Sin 8 Sun Samu Karuwar GDP Da Kaso Sama Da 5 Bisa Dari A Rubu’in Farkon Bana
- Gwamna Inuwa Ya Bukaci Musulmai Su Ci Gaba Da Habbaka Darussan Ramadana
Lauyan EFCC, Kingsley Kudus, ya nemi kotun da ta ajiye mutanen uku a gidan gyaran hali na Akure yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Ya ce duk da cewa mutanen sun musanta zargin da ake yi musu, har yanzu suna karkashin kulawar kotu yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Lauyan wadanda ake zargin Barista Femi Emodamori ya shaida wa kotun cewa a shirye yake domin fara shari’ar gadan-gadan.
Ya kuma nemi kotun da ta yi watsi da bukatar ajiye wadanda yake karewar a gidan gyaran hali, kamar yadda lauyan EFCC ya bukata, yana mai cewa takardar nemin belin da suke cike tana kan ka’ida.
Ya ƙa6ra da cewa daya daga cikin mutanen da yake karewa na fama da rashin lafiyar da ke bukatar kulawar gaggawa.
Daga karshe dai alkalin kotun mai shari’a Adegboyega Adebusoye ya bayar da belin mutunen tare da dage shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Mayu.