Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labor Party (LP), Peter Obi, ya jajantawa tsohon mataimakin kakakin majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu kam shiga hannun jami’an tsaro da ya yi shi da mai dakinsa a Burtaniya.
Rahotanni sun yi nuni da cewa hukumomi a birnin Landan sun tsare Ekweremadu da mai dakinsa, Beatrice bisa zargin yunkurin cire wani sashi na jikin dan adam.
- LEADERSHIP Ta Cika Shekara Daya Da Fara Gabatar Da Shirye-shiryen PODCAST
- Birnin Legas Ya Zama Na Biyu Mafi Muni Wajen Yin Rayuwa A Duniya
A ranar Alhamis aka gurfanar da su a wata kotun Majistare, inda kuma aka kiba da belinsu kana kotun ta dage karar zuwa 7 ga watan Yuli.
Rahotannin da jami’an tsaron birnin na Landan suka fitar, sun nuna cewa an kama Ekweremadu da matarsa bisa zargin yunkurin cire wa wani yaro wani sashi na jikinsa.
Bayanan sun bayyana cewa Ekweremadu yana da wata ‘ya mai larura da ke bukatar koda, wanda ake zargin ta yaron za a cire a dasa mata.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Obi ya ce sun dukufa wajen yi wa Ekweremadu da mai dakinsa addu’a wajen ganin ‘yarsu ta samu lafiya.
“Ni da iyalina, muna tare da Ekweremadu kan halin da ya shiga. Za mu dukufa wajen yin addu’a domin fatan Ubangiji ya ba ‘yarsu lafiya ya kuma tabbatar da adalci.” In ji Obi.