A Indiya, laifukan batsa da ake aikatawa a bainar jama’a na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce.
kayataccen jirgin kasan Indiya na zamani, ma cike da na’urorin sanyaya daki, wanda ke zarga-zirga a fadin kasar, na neman zama wani dandali na bayyana soyayya tsakanin masoya.
Wani bidiyon da ya bulla a makon da ya gabata wanda ke nuna yadda wasu ma’aurata ke sunbatar juna a cikin jirgin kasan a birnin Delhi ya haifar da ce-ce–ku-ce bayan bullarsa a shafukan sada zumunta.
A cikin bidiyon an ga matar na kwance a kan cinyar mijin nata a lokacin da suke sunbatar juna.
Lamarin ya sa ma’aikatar sufurin jiragen kasar ta kasar ta bukaci fasinjoji da su rika kai rahoton duk wani abu da suka ga ya saba al’adun kasar a lokacin da suke cikin jirgi.
Hukumar ta kuma alkawarta cewa za ta kara yawan ma’aikatan jirgi da za su rika lura da ire-iren wadannan laifuka.
Bidiyon da kuma sukar da ya fuskanta a shafukan sada zumunta sun haifar da muhawara kan tsarin tarbiyya a kasar.
Alal misali, wasu daga cikin sakonnin da aka aike wa hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Indiya ta hanyar shafukan sada zumunta sun nuna rashin jin dadi game da hakan.
Haka kuma jirgin kasan na neman zama wani dandali da mutane ke aikata laifukan da ke da alaka da batsa.
A watan da ya gabata wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna wani saurayi na wasa da al’aurarsa a cikin jirgin a birnin Delhi.
Lamarin da ya janyo ma’aikatar al’amuran mata fitar da wani gargadi.
Yayin da mutane da dama ke kallon wasa da al’aura a matsayin laifi, wanda hakan zai iya haifar da laifukan da suka shafi zina, ko tayar da sha’awa, musamman idan ana yinsa a bainar jama’a.
A shekarar 2018, wasu fusatattun fasinjoji sun daki wasu ma’aurata saboda sun rungumi juna a bainar jama’a a birnin Kolkata na Gabashin kasar.
Lamarin ya tayar da kura sosai a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke kira ga jama’a da su daina daukar doka a hannu musamman kan ma’aurata matasa.
A shekarar 2019, wani bidiyon da aka dauka da kyamarorin tsaro na CCTB ya nuna wasu ma’aurata na saduwa da juna a tashar jirgin kasa da ke birnin Delhi, bidiyon da shi ma ya tayar da kura a shafukan sada zumunta.
Shin sunbata na iya zama laifin batsa?
A shekarar 1981, lokacin da Yarima Charles ya ziyarci inda ake daukar fina-finan Indiya, tauraruwar fina-finan Indiya Padmini
Kolhapure ta tarbe shi da chinkon fure tare da sunbatar kuncinsa.
Wanna ya sanya ta zama fitacciya a matsayin ”Mace guda da ta taba sunbatar Yarima Charles”, duk da ta fada a wata hira da aka yi da ita a shekarar da ta gabata cewa wannan ba ”wani abu” ba ne.
To amma hakan na iya zama wani abu.
A shekarar 2007, an zargi tauraron Hollywood Richard Gere da cin mutuncin al’adun Indiya, bayan ya sunbaci tauraruwar Bollowood Shilpa Shetty a kuncinta a lokacin wani taron wayar da kai kan cutar AIDS.
Gere ya ce ya yi hakan ne don ya nuna wa mutane cewa sunbata ba ta sa mutum ya dauki cutar AIDS, to sai dai an zargi ita tauruwa Shetty da cewa ta aikata laifi, saboda suntabarta da aka yi a bainar jama’a.
A lokacin da kotu ta wanke Shetty daga zargin a shekarar 2022, kotun ta ce ba laifinta ba ne, saboda ba ta son cewa Gere zai sunbace ta ba.
A shekarun da suka gabata, sunbatar juna tsakanin ma’aurata ko masoya ya zama ruwan dare musamman a fina-finan kasar.
To amma a kasa mai yawan al’umma kamar Indiya, inda mafi yawan matasa ke rayuwa da iyalansu, batun sirri wani babban al’amari ne.
Ma’auratan da ke kokarin kebanta domin samun sirri kan fuskanci cikas, inda wasu otal-otal a kasar ke neman ganin takardar shaidar aure kafin bai wa ma’aurata daki a otal.
Dokokin Indiya sun tanadi hukunci kan duk mutumin da ya nemi yin abubuwan da za su iya janyo batsa a bainar jama’a, ciki kuwa har da wakokin batsa.
To dai hukunce-hukuncen kotuna da dama a kasar sun nuna cewa sunbata a bainar jama’a ba zai zama laifin batsa ba.
Wani lauya da ya kare wasu ma’aurata a shekarar 2018 ya ce sunbata a bainar jama’a kan zama laifi ne kawai idan an yi ta da nufin tayar da sha’awa.
\
Mun samo muku daga BBC HAUSA