• English
  • Business News
Sunday, September 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ranar Yaki Da Shaye Shaye Ta Duniya: Dr. Fauziyya Ta Tunatar Da Iyaye Aikin Dake Gabansu

by Abdullahi Muh'd Sheka
3 years ago
in Rahotonni
0
Ranar Yaki Da Shaye Shaye Ta Duniya: Dr. Fauziyya Ta Tunatar Da Iyaye Aikin Dake Gabansu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ranar 26 ga wata June ne Majalisar Dunkin duniya ta ware domin yin Nazarin Kan Matsalar shaye shayen miyagun Kwayoyi a tsakanin al’umma.

mashawarciya ta musamman Kan Harkokin Lafiya ga Gwamna Ganduje, Shugabar Kwamitin Yaki da shaye-shaye ta Jihar Kano sannan kuma Shugabar Kwamitin Lura da masu cutar kwakwalwa Dr. Fauziyya Buba Idris ce ta bayyana Haka alokacin taron Manema labarai data gudanar a ofishinta.

  • Majalisar Malaman Musulunci Ta Oyo Sun Nada Ganduje Sarautar ALAUDDEN Na Yarbawa

“Sanin kowa ne yadda Annobar Korana ta haifarwa da Duniya mummunar matsàla da har yanzu kokarin farfadowa ake daga illar da annobar ta yiwa duniya. Wannan ne babban dalilin da yasa dole a yiwa Matsalar shaye shayen Miyagun Kwayoyi kallon tsanaki tare da hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki domin fatattakar wannan matsala da ahalin ke neman zamewa al’umma babban kalubalen.

Dr. Fauziyya Buba Idris ta ci gaba da bayyana cewa wannan Rana Ce da Majalisar duniya ta ware domin yin Nazarin tare da bincika yadda za’a dakile wannan annoba ta shaye shayen Miyagun Kwayoyi da yanzu ke neman Zama wata gagarumar matsàla tsakanin matasa maza da matan wannan lokaci. Tace lamarin na tayarwa da duk wani Mai kishin cigaban al’umma hankali.

Hakazalika Kwararriyar masaniyar matsalolin Mata (Gani) ta bayyana cewa duk matsalolin Da ahalin yanzu Suka addabi Jama’a Ba su Wuce wannan Matsalar ta shaye shaye ba, “Idan aka tsinci Kai a irin wannan matsala daga ita ne ake fadawa sace sace, Matsalar Daba, fashi da makami, Garkuwan da Mutane fyade da sauransu.

Labarai Masu Nasaba

Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

Tace domin Kawo karshen wannan matsala a Jihar Kano, Gwamna Dakta Abdullahu Umar Ganduje ya kafa wani kwakkwaran Kwamitin Mai mutanen 11 wadanda suke aiki ba dare ba Rana Wajen zakulo hanyoyin dakile yaduwar wannan mummunar ta’ada. Zuwa yanzu alhamdulillahi ana samu gagarumin ci gaba a aikin da ake na magance wannan matsala.

Taken taron na bana shi ne “Ya Za’ayi a samu hanyar Warware wannan matsala Baki Daya” yin hakan Kuma aiki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa da ake Bukatar Hana hannu domin dakile wannan annoba. Don Haka sai ta shawarci iyaye dasu Kara kaimi Wajen Lura da wadanda yaransu ke mu’amala dasu domin gudun kitso da kwarkwata.

Saboda kyakkyawan fatan da ake dashi, Gwamnatin Jihar Kano ta kafa Kwamitocin tun daga matakin Kananan Hukumomin har zuwa mazabu, wanda kowa ne magidanci zai iya zuwa domin samun Karin haske akan wannan lamari tare da sanar da hukumomi irin halin da wasu yaran ke ciki.

A karshe Dr. Fauziyya ta jinjinawa kokarin da Gwamnati keyi na dakile wannan annoba, sannan ta godewa iyayen Kasa bisa hadin Kan suke bayarwa aduk lokacin da Bukatar Haka ta taso, musamman batun fadakarwa da Wayar da Kan Jama’a Baki Daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Hajjin Bana: Gwamna Bagudu Ya Nada Ministan Shari’a Amirul-Hajj Na Jihar Kebbi

Next Post

Dalilan Da Ya Sa Muka Halatta Sayen Bindiga Don Kare Kai —Gwamnatin Zamfara

Related

'Yan Bindiga
Rahotonni

Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina

2 days ago
Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
Rahotonni

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

1 week ago
Sin Ta Fara Amfani Da Tauraron Dan Adam Wajen Duba Manyan Hanyoyin Wutar Lantarki A Karo Na Farko
Rahotonni

Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago

1 week ago
Akwai Bukatar Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Legas Wajen Bunkasa Albarkatun Fatu
Rahotonni

Akwai Bukatar Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Legas Wajen Bunkasa Albarkatun Fatu

1 week ago
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya
Rahotonni

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

2 weeks ago
Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari
Rahotonni

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

2 weeks ago
Next Post
Dalilan Da Ya Sa Muka Halatta Sayen Bindiga Don Kare Kai —Gwamnatin Zamfara

Dalilan Da Ya Sa Muka Halatta Sayen Bindiga Don Kare Kai —Gwamnatin Zamfara

LABARAI MASU NASABA

ASUU

Malaman Jami’o’i Sun Zama Abin Tausayi —Kungiyar ASUU

September 7, 2025
Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya

Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya

September 7, 2025
Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63 

Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63 

September 7, 2025
Mun Tara KuÉ—i Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 

Mun Tara KuÉ—i Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 

September 7, 2025
Fyade

Matsalar Ciwon Kwakwalwa A Gidajen Yarin Kasar Nan

September 7, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Sake Maido Da Ma’aikatar Yaki A Amurka Ya Nuna Babu Dakatawa A Yaki Hatta A Wajen Sa Suna 

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Sake Maido Da Ma’aikatar Yaki A Amurka Ya Nuna Babu Dakatawa A Yaki Hatta A Wajen Sa Suna 

September 6, 2025
Rikicin NNPP A Kano: Wani Tsagi Ya Soki Korar Abdulmumini Jibrin Kofa

Rikicin NNPP A Kano: Wani Tsagi Ya Soki Korar Abdulmumini Jibrin Kofa

September 6, 2025
Koyo Daga Tarihi Da Kiyaye Zaman Lafiya Za Su Sa Kaimi Ga Zamanantar Da Duk Duniya Baki Daya

Koyo Daga Tarihi Da Kiyaye Zaman Lafiya Za Su Sa Kaimi Ga Zamanantar Da Duk Duniya Baki Daya

September 6, 2025
Neman Gurbin Kofin Duniya: Arokodare Ya FarfaÉ—o Da Mafarkin Nijeriya A Wasan Rwanda

Neman Gurbin Kofin Duniya: Arokodare Ya FarfaÉ—o Da Mafarkin Nijeriya A Wasan Rwanda

September 6, 2025
Babban Taron MDD Ya Zartas Da Kudurin Hadin Gwiwar MDD Da SCO

Babban Taron MDD Ya Zartas Da Kudurin Hadin Gwiwar MDD Da SCO

September 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.