Gabanin shiga zaben Majalisar Dokokin kasar nan karo na 10 a ranar Talata 13 ga watan Yuni 2023, gwamnonin jihohi akalla 25 ne suka zabi Sanata Godswill Obong Akpabio, da Sanata Jibrin Barau a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakin shugaban majalisar dattawa na majalisa ta 10.
Gwamnonin sun hada kai da zababbun Sanatoci na manyan jam’iyyu uku: APC, PDP da kuma jam’iyyar LP domin mara wa ‘yan takarar baya.
- Sin Ta Bude Ofishin Jakadanci S Kasar Honduras.
- Xi Jinping: Ana Kokarin Yaki Da Yaduwar Hamada A Sin Don Bude Sabon Babi
Daga cikin gwamnonin guda 25 da ke goyon bayan Akpabio sun hada da Gwamnonin Kwara, Nasarawa, Benue, Ogun, Oyo, Legas, Ekiti, Osun, Kogi, Ribas, Kuros Riba, Kaduna, Borno, Ebonyi da kuma Ondo.
Gwamnonin, wadanda akasarinsu na Jihohin da ke karkashin Jam’iyyar APC ne, sun ci gaba da cewa, sun yi kakkausar suka wajen amincewa da shawarar da Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) na jam’iyya mai mulki ya dauka.
Gwamnonin sun kara da cewa jam’iyyar APC ta yanke shawara mafi inganci da za ta inganta zaman lafiya a hukumomi da kuma gudanar da harkokin majalisa cikin lumana a majalisa ta kasa ta 10 nan da shekara hudu masu zuwa.
Musamman a lokacin da Akpabio ya ziyarci Gwamna Yahaya Bello a Jihar Kogi, gwamnan ya bayyana burin Akpabio da Barau na lashe kujerun shugaban majalisar dattawa da mataimaki a majalisa ta 10.
Ya kuma bayyana cewa Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja-Delta, shi ne abin koyinsa, inda ya kara da cewa salon mulkin Sanatan da ba a saba gani ba a matsayinsa na gwamnan Jihar Akwa Ibom, ya sa ya so ya zama kamar tsohon gwamnan.
Gwamnan Kogi ya ce zai yi kokarin ganin an samu kwanciyar hankali a fadar shugaban kasa Bola Tinubu.
Har ila yau, gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya ce zababbun sanatoci da sauran masu ruwa da tsaki a jihar ne ke goyon bayan takarar Sanata Akpabio don ya gaji Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kuma bayyana cewa gwamnonin APC na Arewa cewa sun kuduri aniyar mara wa shugaba Bola Tinubu baya na zaben shugabannin majalisar dokokin kasar nan.
Gwamna Babajide Sanwo a Jihar Legas ya ce yana fatan Majalisar ta 10 za ta kasance ne kan “Sarfafa sabbin dokoki” don inganta abubuwan da aka riga aka yi a Majalisar ta tara.
Ya bayyana kungiyar zababbun Sanatoci a fadin jam’iyyar a matsayin “kungiyar da ta yi aiki sosai”.
Har ila yau, wata majiya ta kusa da Gwamnonin APC ta yi nuni da cewa, suna sa ran ganin an samu zaman lafiya, kwanciyar hankali a zauren majalisar ta 10.