Kungiyar kwallon kafa ta West Ham United da ke Ingila ta lashe kofin Uefa Conference League bayan doke Fiorentina da ci 2-1 a wasan karshe da suka buga a birnin Prague na kasar Czech Republic.
Said Benrahma ne, ya fara jefa kwallo a minti na 62 bayan samun bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan da alkalin wasa Del Cerro Grande ya yanke hukunci.
- Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 26 A Kan Roka Daya
- ‘Yansanda Sun Rufe Majalisar Dokokin Nasarawa Kan Rikicin Shugabanci
Bonaventura ya farke wa Fiorentina kwallo a minti na 67, kafin Bowen ya jefa wa West Ham kwallo ta biyu a minti na 90.
Hakan ya sa kungiyar da ke Landan ta lashe kofi a karon farko bayan shekaru 43.
Kazalika, David Moyes ya lashe Kofi a karon farko a shekaru 25 da ya shafe yana horarwa.
Kyaftin din kungiyar Declan Rice wanda ka iya buga wasansa na karshe, shi ma ya dauki kofi na farko a tarihinsa.