Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 65 ga maniyyatan jihar 6,166, wadanda suka yi aikin hajjin 2023 a kasa mai tsarki.
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata yayin taron bayan gudanar da aikin hajjin a Makka.
- Tinubu Ya Yi Ganawarsa Ta Farko Da Hafsoshin Tsaro
- Hajjin Bana: Abin Da Ya Sa Alhazan Nijeriya 14 Suka Rasu
Ya ce kowane mahajjaci za a ba shi Riyal 50.
Babban Darakta ya bayyana cewa an yi hakan ne don kyautatawa mahajjatan a kasa mai tsarki.
Ya bukaci alhazan da su kashe kyautar kudin ta hanyar da ta dace.
Daga nan ya bukaci alhazan da su ci gaba da kokarin nuna kyakykyawan halaye a kasa mai tsarki.
Ya ce, “Alhazai za su dawo daki-daki kamar yadda suka zo kasa mai tsarki.”
Danbappa ya bayyana cewa hukumar za ta fara bayar da buhunan kilo 32 ga maniyyatan jihar Kano tare da kyautar Sallah da gwamna ya bayar.
Babban Daraktan ya bukaci alhazan da su kasance masu hakuri da kuma yi wa Nijeriya da jihar Kano addu’a musamman domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Danbappa ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi aikin hajjin su ya kuma mayar da su gida lafiya.