Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jiha da ke zamanta a Kano, ta yi fatali da karar da jam’iyyar APC da dan takararta Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya suka shigar a gabanta na kalubalantar nasarar dan majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da mazabar tarayya ta Bunkure a majalisar wakilai ta kasa, Kabiru Alhassan Rurum yayin zaben 2023.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa kotun a ranar Litinin ta bayyana cewa masu korafin ba su iya gabatar da wasu kwararan hujjoji a gaban kotun ba domin tabbatar da ikirarin da suka yi kan wanda ya lashe zaben.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji
- Abba Ya Sake Nada Sheikh Daurawa Shugaban Hisbah Ta Kano
Kotun ta jaddada cewa sun kuma gaza wajen bayar da shaida kan zaben 2023 kamar yadda suka yi zargin.
Sai dai kotun ta bai wa masu korafin wa’adin makonni biyu su daukaka kara kan hukuncin da ta yanke idan ba su gamsu da shi ba.
Hukuncin kotun dai shi ne hukunci na farko da aka yanke tun bayan babban zaben 2023.