A makon da ya gabata ne, sakatariyar baitul malin Amurka Janet Yellen ta kammala ziyarar aiki na kwanaki hudu da ta kawo kasar Sin. Kafin ziyararta, shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya kawo makamanciyar wannan ziyara a kasar Sin, ziyarar da ake ganin za ta kara yaukaka alaka tsakanin kasashen biyu.
A yayin shawarwarinta da bangaren Sin, sassan biyu sun bayyana aniyarsu ta karfafa cudanya da hadin gwiwa. Sai dai wannan ba shi ne karon farko da ake jin kasashen biyu na furta irin wadannan kalamai ba, amma daga karshe sai a wayi gari Amurka ta sa kafa ta yi fatali da abin da aka cimma, matakin dake sake mayar da hannun agogon baya a hadin gwiwar kasashen dake zama mafiya karfin tattalin arziki a duniya.
Idan ba a manta ba, ko shi ma Blinken ya furta irin wadannan kalamai na karfafa alaka da mutunta alkawuran da aka cimma, amma bayan komawarsa gida, sai aka ji shi yana furta wasu kalamai marasa dacewa game da alakar sassan biyu, Hali aka ce zanen Dutse, Ita ma Yellen ta bayyana wasu manufofin Amurka da ba su dace ba, ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa. Tana mai cewa, wai za ta fito da wani tsarin tattalin arziki mai adalci, wannan shi ne an bai kura fida.
Masu fashin baki dai na cewa, har yanzu akwai bambance-bambance tsakanin kasashen biyu ta fuskar inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, don haka ya dace Amurka ta kara kokari da nuna sanin ya kamata ta kuma cika alkawuran da ta yi, tare da daina kakabawa Sin takunkuman da ko kadan ba su dace ba.
Duniya dai ta zuba idon tare da fatan gwamnatin Amurka, za ta dauki hakikanin matakai domin ciyar da huldarta Sin gaba yadda ya kamata, wadda ke da muhimmanci ba ma ga kasashen biyu ba, har ma ga duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)