Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa ofishin jakadancin Nijeriya na Birtaniya ya dauki lauyoyi da za su kare Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, wadanda a halin yanzu ake tsare da su kan zargin su da safarar sassan jiki dan Adam.
Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da ya ke bayar da cikakken bayanin ganawar sirri da majalisar ta yi kafin fara zaman majalisar.
- Ukraine Na Bukatar Dala Biliyan Biyar Domin Yakar Rasha A Kowanne Wata
- Takardun Karatuna Kaf Sun Bata — Kabiru Masari
A cewar Lawan, wata tawaga daga kwamitinta mai kula da harkokin kasashen waje za ta tashi daga Nijeriya zuwa Landan a ranar 1 ga watan Yuli, 2022, domin kai ziyara ga Sanatan da ke cikin tsare.
Ya kara da cewa matakin da aka dauka na shiga maganar ta kama Ekweremadu da tsare shi ya zo ne sakamakon rahoton da babban jakadan Nijeriya a Landan ya samu.
Ya kuma bayyana cewa majalisar dattawa za ta tuntubi ma’aikatar harkokin wajen kasar da kuma ofishin jakadancin Nijeriya da ke Landan kan kama Sanata Ekweremadu da ‘yan sandan birnin Landan suka yi a kwanakin baya.
“Na yi ganawar sirri da babban kwamishinanmu na Nijeriya a Birtaniya, Alhaji Isola Sarafa, wanda ya yi matukar kokari wajen kulla alaka da abokin aikinmu, wanda ya samu nasarar shigar da tawagarsa a kotu da ke Uxbridge inda Ekweremadu yake”