Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira. Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da batun da wasu mutanen ke cewa; iya kwalliya da iya magana kadai ke janye hankalin namiji a wajen mace, musamma matan aure. Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu, ko wadanne abubuwa ne ke janyo hankalin namiji ga matarsa? Me yake janyo wa wasu matan wadanda sun san hanyoyin da za su bi dan janyo hankalin mazajensu, amma kuma ba sa iya yi? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Musbahu Muhammad daga Goron Dutse Kano:
Ba haka ba ne akwai dalilai da yawa amma suma suna daga ckin abin da Mata suke so a zamantakewar aure. Abubuwan da ke Janye hankalin mazan Aure shi ne; Hankali, Biyayya, Tausayawa, Soyayya da kuma biyan bukatar Aure. Rashin Juriya da Yawan Addu’a shi ke kawo hakan. Ya kamata su sani cewa duk abin da za su yi su janye hankalin mazajensu tofa lada za su samu domin Aure Ibadah ne, sannan yin hakan zai sa Namiji ya kame game da kule kulen mata a waje.
Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Hakuri ya kamata ya zo akan gaba, sannan tsafta da iya magana su biyo baya, domin duk tsaftarki idan baki da hakuri ba zai yi wani tasiri a wurin miji ba. A tunanina idan har akwai kauna a dukkan bangarorin biyu sai kuma ya zama akwai kyautatawa juna tare tsafta da kwalliya shi ne za a samu dankon kyauna har ma namiji ya mance da ta waje, tabbas! akwai matan da sun san yadda za su ja hankalin mijin amma ba sa yi, wannan baya rasa nasaba da gazawan wasu mazan wajen kasa kyautatawa iyalinsu koda ace tana son ta burge mijin sai ya kasance kullum zuciyarta akwai zafin shi babu yadda za a yi ta iya, domin shi ma bai burgeta ba bare tayi kokarin burge shi, abin da nake son in nuna anan sai an samu daidaito daga bangarorin biyu kafin zaman yayi karko, ya zama daga mijin har matar kowa na iya bakin kokarin shi.
Sunana Rabi’atu Abdullahi Aminu daga Jihar Kano:
A gaskiyar batun ba wai iya kwalliya da iya Magana kadai ke jan hankalin namiji zuwa ga mace ba musamman ga matan aure, akwai abubuwa da yawa da suke jan hankalin namiji zuwa ga matarsa wanda ciki akwai iya kwalliyar da kuma iya maganar, amma ba za a ce sune kadai ba dan akwai muhimman dake gabansu. Abubuwan dake janye hankalin miji zuwa ga matar sa na da yawa misali; akwai Tsafta, wadda tana cikin jigajigan zaman aure, biyayya, Hakuri, Girki, Iya kwalliya, Iya sarrafa harshe wajen magana, da kuma girmamawa. Wadannan sune abubuwan dake jan hankalin namiji zuwa ga matar sa ya kuma kara musu dankon so da kaunar juna. Akwai matan da sun san yadda za su janyo hankalin mazajensu amma basa yi saboda wasu dalilai nasu na daban wanda jigo shi ne; Rashin so ga wadanda aka yi wa auren dole, ko kuwa malalaciyar mata me son jiki. Shawarata ga matan da suka san yadda za su janyo hankalin mazajensu amma ba sa yi shi ne ke malalaciya ki farka daga barci da kike yi dan kuwa kina wannan lalacin naki zai fita waje ya samo me yi masa abin da ke kika kasa saboda san jiki, gwara ki gyara ba sai yayi aure ba ki ce ta mallake shi alhalin iya tafiyar da shi kawai ta fiki ba kuma dan rashi sani ba, sai dan san jiki mara amfani. Ke kuwa me ihun ai auren dole ne ya kamata ki zubda makamanki domin aure dai an riga an daure, gwara ki hakura ki karbi kaddararki ki daura damarar rike mijinki ta yadda gidan aurenki zai zama wajen farin cikinki da kwanciyar hankali ba wai damuwa ba. Allah ya sa mu dace Ameen.
Sunana Lawan Isma’ila (Abu Amfusamu)
Maganar gaskiya ba iya sune kadai suke iya jan hankalin da namiji ga macen aure ba. 1. Akwai tsafta 2. Da iya furta kalamai 3. Da kuma tausayi, domin a wannan zamanin indai har za kina tausayawa mijinki a kan yadda yake tafiyar da rayuwar iyalinsa za ki sha mamaki wajen baki kulawa koda ace kin san yana da shi (kudi) sabida sune dai kusan suke tafiyar da mafiya yawancin uzururrukanmu na yau da kullum, duba da yanzu komai yayi tsada to in sha Allahu za ku zauna lafiya da shi mai gidanki da sauransu, duba da a takaice aka ce amma suna da yawa. Kulawa zai tafi a dawo lafiya, idan ma da hali ana rakashi haka idan ya dawo, sannan wancan magana din ta wanka koma nace tsafta gabaki daya da iya furta kalamai na fira da kuma furta magana wajen neman wani abu daga wajen namiji. Wasu girman kai ne wanda suke amfani da kalaman wasu matan da suke cewa idan kin fiye yi wa namiji biyayya to za ki kwana a ciki suna manta cewa Allah ne ya dora maza akan mata da sauransu. Shawarata anan ita ce suyi hakuri su gyara sabida aure biyayya ne, sannan suna tuna cewa bauta suke yi, sannan duk wani abu da ya mance tayi a gidan mijinta indai bai sabawa shari ai ko mijin nata ba to ta sani aikin lada ne a gunta kada ta biyewa wasu matan wannan zamanin.
Sunana Hajara Ahmad (Oum-Nass) Daga garin Hadejia a Jihar Jigawa:
Gaskiyar batu za a iya cewa kwalliya da iya magana na cikin jerin abubuwan da sukan yi tasiri a rayuwar zamantakewar aure, amma ba za a ce sune ginshikin da ke janye hankalin namiji zuwa ga mace ba, domin maza kala-kala ne kowanne a ciki kuma akwai abin da yake so a tare da matarsa. Ladabi da biyayya, da hakuri, kawaici, iya girki, sai kwalliya da iya maganar da aka ambata a baya, girmama abin da yake so, da kuma gujewa abin da ba ya so, kaunar ‘yan uwansa, mayar da shi abokin shawara da kuma abokin wasa. Wadannan suna cikin shika-shikan abubuwan da ke jan hankalin maza. Wasu matan akwai girman kai a cikin lammuransu, wasu kuma tsoro ne na rashin ba su saba ba, wasu kuma suna ganin idan sun yi kamar mijin zai iya kushe su ne. Wadannan za su iya zama dalilan da ke hana mata nuna soyayyarsu da kulawarsu ga mazajensu. A ganina su yi kokari su gyara, domin yanzu an zo wani irin zamani ne da matan waje ke wawason maza, idan ke matar gida ba ki killace mijinki ba, kina ganin zai miki nisa. Kuma a batun aure babu kunya babu boye-boye domin kun zama daya, don haka mafitar gyaran aurenki na hannunki, kunya, girman kai, tsoro, duk ki kawar da su ki rungumi mijinki da soyayya.
Sunana Nazifi Ahmad Chikawa daga Chikawa, Madobi Jihar Kano:
Tabbas iya tsara kwalliya da kuma iya tsara kalamai masu jan hankali ga mace suna jan hankalin namiji sosai zuwa ga mace. Amma ba su kadai ba ne, domin abubuwan da ke janye hankalin namiji zuwa ga mace suna da yawan gaske. Abubuwan suna da yawa; amma wadanda suka fi tasiri musamman a wannan zamanin su ne kamar irinsu; Shagwaba, tsafta, kwalliya, hakuri, girmamawa, da kuma jure dukkan wata damuwarsa a koda yaushe musamman wajen saduwar aure. Da dama daga cikin mata suna ganin idan kika cika yi wa namiji biyayya zai rainaki, ko kuma ajinki zai ragu a wajensu. Hakan na janyo wasu matayen su ki bawa mazajensu cikakkiyar kulawar da za ta saka su ji duk duniya babu wacce suke so da kauna sama da su. Wasu matayen kuma rashin wayewa ne ke damunsu ko kuma kunya wadda bata da amfani. Shawara mafi muhimmanci ita ce; duk wata hanya da mace ta san mijinta ya fi bukatar kulawa to ta kasance ta kware a wannan fannin. Ta zama gwana a duk abin da mijinta ya fi so kamar kwalliya, girmamawa, iya girki, tsafta, kiyaye hakkin aure. Sannan mace ta cire dukkan kunya ta tarairayi mijinta cikin kissa da kisisina da Shagwaba.
Sunana daga Habiba Mustapha Abdullahi (Dr.Haibat) daga Jihar:
A gaskiyar magana wannan magana haka take iya magana takan samu wanin matsayi ne ba ma miji ba koda a ko Ina ne kula da duk wani abin da ya fi so ko ta fannin girki ko ta fannin soyaya ko ‘yan uwansa ko tafiya. A gaskiya yin haka ba daidai bane ko mai mijinka zai yi ka da ka bari ya shafi soyayya ka. Dan Allah ‘yan uwana mata mu gyara hakan, duk matar da ta san hanyoyyin faran tawa mijita muna mutukar samu farin cikin a cikin gida musamman wajen zaman aure saboda da shi aure wata dama ce ko kuma hanya ce ta samun faran tawa juna da nunawa juna kololuwar soyayya.
Sunana Ibraheem Ismail Ibraheem daga Jihar Kano:
Eh! Gaskiya haka ne maganar, shi rai yana son mai kyautata masa kuma da mai tsafta abu na farko shi ne iya kwalliya, tsafta, rikon amana da bada kulawa indai mace za ta zamo mai yi to namiji zai ji yana masifar kyaunarta matan da suka san yadda za su yi su janyo hankalinsa mutukar ta kasa yi to gaskiya laifinta ne dan ya je waje ya ga wata ya nuna yana so. Amma shawara daya shi ne; kawai su dauko hanyar da suka san idan sun yi wa namiji abu zai ji dadi dan a rayu cikin so da mutunta juna.