Harry Maguire ya ce kociyan kungiyar Erik ten Hag ya tube shi daga mukamin kyaftin din Manchester United
Tsohon Kocin Man Utd Ole Gunnar Solskjaer ne ya nada Maguire a matsayin kyaftin a watan Janairun 2020 watanni biyar bayan zuwansa daga Leicester City
Dan wasan bayan Ingila ya ce ya ji takaici matuka amma zai ci gaba da bada himma a kungiyar
Dan wasan mai shekaru 30 ana alakanta shi da komawa West Ham
Maguire ya buga wasanni 31 daga cikin 62 da kungiyar ta buga a dukkanin gasa a kakar bara, wanda kwantiraginsa a Old Trafford zai kare zuwa 2025
Bayan tattaunawa da manajan a yau ya sanar da ni cewa zai canza kyaftin a kungiyar,Maguire ya wallafa a shafinsa na sada zumunta
Ya bayyana min dalilansa kuma duk na aminta da Bukatar sa
Ina so in yi godiya ga magoya bayan Manchester United saboda goyon bayan da suka ba ni yayin da nake sanye da kyallen kyaftin
Tun daga ranar da na É—auki aikin, shekaru uku da rabi da suka wuce ina matukar alfahari da jagorancin Manchester United
Kuma yana É—aya daga cikin abubuwan alfahari na rayuwata har zuwa yau
Na yi duk abin da zan iya don taimaka wa United ta yi nasara a ciki da wajen fili
Raphael Varane da Lisandro Martinez an fifita su kan Maguire a tsakiyar tsaron United a kakar wasan da ta gabata, kuma lokacin da dan wasan ya ji rauni, Victor Lindelof ya maye gurbinsa