Wata Babbar Kotun Tarayya ta bai wa Gwamnatin Kano umarnin biyan tarar naira miliyan biyu saboda yunkurin rushe wasu gine-gine.
Kotun dai ta umarci Gwamnatin Kano da ta biya wasu mutum biyu naira miliyan daya-daya saboda yunkurin rushe gine-ginensu a Unguwar Salanta da ke jihar.
- Halin ‘Yan Siyasa Na Ba Sarakuna Mamaki – Sarkin Zazzau
- Masana : Darussa Daga Shirin Kawar Da Talauci Na Kasar Sin Na Da Muhimmanci Ga Afrika
Alkalin da ya jagoranci zaman kotun a yau Juma’a, Mai Shari’a Simon Amobeda, ya ce Gwamnatin Kanon ta sauka daga kan layi ta daidai saboda shafa wa gine-gine fenti mai nuna alamar rusau kan zargin an yi su ne ba bisa ka’ida ba.
Mai Shari’a Simon ya kafa hujjar cewa, Gwamnatin ta saba wa sashe na 43 da 44 da ya bai wa wadanda abin ya shafa — Saminu Shehu Muhd da Tasiu Shehu Muhammad — ’yancin mallakar gine-gine kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadar.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, gine-gine da lamarin ya shafa sun hada da fulotai masu lamba 41 da 43 da kuma 68 a Unguwar Salanta.
Kazalika, kotun ta riki cewa kutse da Gwamnatin Kanon ta yi a gine-ginen da misalin karfe 11 na daren ranar 14 ga watan Yunin 2023 ya saba wa tanadin Kundin Tsarin Mulkin na Kasa.
Kotun ta kuma bai wa Gwamnatin Kano umarnin sake fentin gine-ginen wanda Hukumar Tsara Birni ta Kano KNUPDA ta shafa wa alamar mai dauke jan fenti.
Da yake batu bayan hukuncin, Barista Bashir Ibrahim wanda ya shigar da kara a gaban kuliya, ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke a matsayin abun yabawa saboda kare ’yanci da martabar bilAdama.
A nasa bangaren, Lauyan Gwamnatin Kano, Barista Musa Dahuru Muhad, ya ce za su yi nazari kan hukuncin da kotun ta yanke gabanin daukar matakin da ya dace.