Wasu masana a fannin noman Rogo a kasar nan, sun bayyana cewa, bukatar da ake da ita ta Rogo don sarrafa shi zuwa sauran nau’ukan abinci ya kai tan miliyan 300,000 a duk shekara.
Sun bayyana hakan ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki a fannin da suka gudanar a babban birinin tarayyar Abuja.
- Rikicin Nijar: Tinubu Ya Aika Janar Abdulsalami, Sultan Na Sokoto Zuwa Yamai
- Chelsea Ta Dauki Mai Tsaron Raga Daga Brighton
A cewarsu, samar da shi ya kai kasa da tan 10,000 tonnes; haka ana kara bukatar Rogon wajen sarrafa magunguna da suka kai sama da tan 350,000.
Sun kara da cewa, karin bukatar da ake da ita ta man da ake samu da ake kiransa a turance ethanol da ake yin amfani da shi wajen girki da kuma wanda ake sanya wa ababen hawa wato a kasar nan ya karu zuwa lita biliyan daya.
“Samar da shi ya kai kasa da tan 10,000 tonnes; haka ana kara bukatar Rogon wajen sarrafa magunguna da suka kai sama da tan 350,000.”
Masanan sun ci gaba da cewa, sama da kadada miliyan 24 ake noman Rogo a kasashe 106, inda suka bayyana cewa, Nijeriya ke a kan gaba wajen samar da shi.
Kazalika, a cewarsu, amfanin ya kasance daya daga cikin amfanin gona da ke kara karfafa tattalin arzikin duniya.
Sun sanar da cewa, bincike ya nuna cewa, Nijeriya a matsayinta ce take kan gaba wajen noman Rogo, inda suka ce, kasar na samar da kimanin tan miliyan 53 na Rogo a duk shekarar.
Sun kara da cewa, kasr na kuma samar da akalla tan 7.7 ako wacce kadada daya.
Sun bayyana cewa, bisa wata kididdigar da aka fitar a kwnan baya, ta bayyana cewa, daga cikin tan miliyan 53 na Rogon da ake noma wa a Nijeriya a duk shekara.
Kazalika sun bayyana cewa, sama da kashi 90 a cikin dari ana sarrafa Rogon zuwa sauran wasu nau’ukan abinci, inda kuma masana’antun da ke sarrafa shi a kasar suke ci gaba da nuna bukatarsa.
Hakazalika, fannin na noman Rogon ya taimaka wajen samar wa da miliyoyin ‘yan Nijeriya aikin yi idan kuma aka inganta fannin, zai samar fiye da hakan.
“Kashi 90 a cikin dari ana sarrafa Rogon zuwa sauran wasu nau’ukan abinci, inda kuma masana’antun da ke sarrafa shi a kasar suke ci gaba da nuna bukatarsa.”
Wasu daga cikin manoman da suka halarci taron na masu ruwa da tsaki a fannin na noman Rogon a kasar nan sun bayyana cewa, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara bunkasa fannin ganin cewa, fanni ne da ke kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
“Nijeriya ta kasance a kan gaba wajen fitar da Rogo zuwa kasar waje, inda kuma hakan ke kara habaka mata kudaden ta ajiya a asusun kasar waje.”
Sun kuna nuna bacin ransu akan yadda Nijeriya ke shigo da Rogon da ya kai na sama da dala miliyan 600 a duk shekara.
“Fannin na noman Rogon a kasar nan sun bayyana cewa, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara bunkasa fannin ganin cewa, fanni ne da ke kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.”
Sun yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar a samo masu zuba dimbin jarinsu a fannin, musamman don a cike gibin bukatar da ake da shi da kuma tura shi.