Nijeriya da Nijar ‘yan’uwan juna ne, ana kuma sa ran za su ci gaba da kasancewa a matsayin ‘yan’uwan junan. Don haka, ka da mu yarda mu rudu da jin cewa muna da karfi ko kwarewa da za ta sa mu afka wa juna ta fuska yaki, musamman idan muka yi la’akari da abin da ya faru da Kasar Ukraine, ya isa mu gane cewa ba a taba yin bari a kwashe duka.
Shugabanci ya kunshi abubuwa da dama da suka hada da samar da masalaha, tuntuba da kuma ba da damar tattaunawa domin samar da maslaha a tsanin bangarori daban-daban. Don haka, idan har muna bukatar ci gaba da zama a matsayin ‘yan’uwan juna, wajibi ne mu ci gaba da aiwatar da harkokinmu a matsayin ‘yan Afrika kuma uwa daya uba daya. kazalika, dole ne mu fahimci yadda za rika zama muna tattaunawa a tsakanin duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
- Yanzu-Yanzu: Masallacin Fadar Sarkin Zazzau Ya Rufta Da Mutane Yayin Sallar La’asar
- Yadda Malamai Suka Dirar Wa Batun Yaki Da Nijar
Haka zalika, ya kyautu a rika baiwa kowa ‘yancin da yake da shi tare da samar da kyakkyawar hanyar tattaunawa a lokacin da ya dace, musamman idan akwai bukatar hakan, ko da kuwa abin da ya shafi kungiyar ECOWAS ne, wannan dalili ne ma ya sa kasashen Afrikan suka shiga wannan kungiya, har ake zaben shugabanni lokaci zuwa lokaci, wanda hakan yasa aka zama kamar uwa daya uba daya.
Bugu da kari, ya zama tilas mu koyi yadda za mu rika warware matsalolinmu a tsakanin mu na mutanen Afrika, duk wani kutse da turawan yamma za su yi a tsakanin mu da sunan taimako, babu abin da zai tsinana mana illa sake jefa mu halin ha’u’la’i. Idan muka yi la’akari da magabatan shugabanninmu na Afrika irin su marigayi Tafawa Balewa, Kwame Nkrumah Julius Nyerere, Milton Obote, Samora Mitchel, Banda, Omar Bongo, Ahamadou Ahidjo, Senghore, Mandela da sauran makamantansu, sun hada kan Afrika tamkar uwa daya uba daya.
Saboda haka, babu yadda za a yi a halin yanzu mu zauna kanmu a rarrabe sannan mu yi tsammanin samun ci gaba ko hadin kai a wadannan yankunan namu na Afrika ba. Don haka, ya kyautu kungiyar ECOWAS ta yi hobasa wajen wanzar da zaman lafiya, hadin kai da kuma kawo ci gaba ga yankunan Afrika tare da sasanta tsakanin ‘ya’yayen nata a matsayinsu na bakar fata, ba wai kasashe irin su Birtaniya, Faransa, Fotigal ko kuma kasashen Larabawa ba, a’a kawai ya kasance Afrika ita ce farko aiwatar da hakan.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Kasar Nijar, kamar abin da ya faru ne a sauran kasashe kamar irin su; Mali, Guinea, Burkina Faso da sauran makamantansu, wanda hakan na nuna baro-baro cewa akwai alamun zalinci tare da cin amanar wadanda suka zabe su, ta hanyar rashin cika alkawarurrukan da suka yi musu, ga kuma uwa-uba bakin talaucin da suke fama da shi sakamakon rikon sakainar kashin da shugabannin nasu suka yi musu. Saboda haka, ya kyautu shugabanni su koyi magana da harshe daya, idan suka fada su rika cikawa.
A halin da ake ciki yanzu, kusan duniya baki-daya na fama da masifu iri daban daban da ya hada da matsalar zaizayar kasa, ambaliyar ruwa, yake-yake da sauran makamantansu. Wadannan dalilai kadai sun isa su sa kungiyar ECOWAS ta shiga hankalinta da kuma sauya tunani. Kasar Nijar babbar garkuwa ce ta fuskar tsaro idan aka yi la’akari da Sahara da take da shi, far mata kan haifarwa kungiyar ECOWAS da mara ido, ta hanyar rikice-rikice tare da bude kofar shigo da makamai wanda hakan kan yi sanadiyar hallaka mu baki-daya.
Don haka, muna kira da babbar murya ga kungiyar ECOWAS, da ta dubi Allah ta samar da hanyoyin warware wadannan matsalolin cikin ruwan sanyi, ba tare da amfani da karfin Soja ba.
Abraham James, Kwararre
ne a kan sadarwa da harkokin Difilomasiyya da ke Nijeriya