Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya yi alkawarin ba da kulawa sosai ga ilimi bisa la’akari da muhimmancinsa ga ci gaban kowace al’umma.
Ya ce a daidai lokacin da gwamnatinsa ta ayyana ilimi a matsayin daya daga cikin ajanda 9 da za ta ba karfi, gwamnatin jihar za ta dauki nauyin ’yan asalin jihar 85 da suka cancanta don yin karatun kwasa-kwasai daban-daban a Jami’ar Arewa maso Yamma (NorthWest), da ke Sokoto.
Gwamna Ahmad Aliyu ya yi wannan alkawarin ne a wajen taron kaddamar da dalibai na shekarar 2022/2023 da aka gudanar a harabar jami’ar da ke kan titin Kalambaina, Sokoto.
Aliyu ya yabawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa kafa jami’ar mai zaman kanta ta farko a jihar.
A nasa tsokaci, Wamakko ya ce manufar kafa jami’ar ita ce ta zama cibiyar kirkire-kirkire da bincike don samar da ci gaba mai dorewa, kiwon lafiya, noma da fasaha a jihar da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.
Ya bayyana jin dadinsa da cewa, jami’ar ta zo a daidai lokacin da gwamnatin jihar mai mulki ta dauki ilimi a daraja ta daya wajen bayar da fifiko.