Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Katsina ta nuna tsananin damuwarta a kan karancin masu fitowa don yankar katin zabe a sabbin runfuna 1,750 da aka kirkiro.
Shugaban hukumar a Jihar Katsina, Alhaji Jibril Zarewa, ya bayyana haka a tattauanwarsa da Kanfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Katsina ranar Juma’a.
- 2023: INEC Ta Kara Wa’adin Ranakun Yin Katin ZabeÂ
- 2023: Kuri’un ‘Yan Nijeriya Ne Za Su Yanke Hukuncin Lashe Zabe – INEC
Ya ce, shekara 1 kekan da fara rajistar sabbin katin zabe amma akwai karancin wadanda suka yi rajista a sabbin akwatunan zaben da aka kirkiro.
Ya kuma kara da cewa, “A watan Mayu na shekara 2022 mun lura cewa, daga cikin sabbin akwatunan zabe 1,750 da aka kirkiro, a akwatuna 1,200 mutanen da suka yi rajista basu wuce mutum 50 ba a kowanne akwati.
“A kan haka muna kira ga al’ummar da aka kirkiro wa sabbin akwati da su garzaya don yin rajista a wuraren don kada a kai ga soke akwatunan.